Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, saboda tsallen da ya tuma daga PDP ya koma APC.
Buhari ya nuna sauyin shekar da Umahi ya yi cewa, “akida ce kawai ta rinjaye shi ya sauya sheka, amma ba wani muradin siyasa ya ke son cimmawa, har ta kai shi ba canja sheka ba.”
“Ina farin ciki da yanke shawarar da Gwamna David Umahi ya yi ya dawo cikin jam’iyyar APC. Wannan kuwa akidar sa ce da tunanin sa, ba wata boyayyar manufa ya ke neman cimmawa ba.”
Haka Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Buhari ya ce, “Shi iya tafiyar da shugabanci nagari ya na da muhimmanci a APC. To ina murna ganin shi wannan gwamna ya fahimci haka, har hakan ya zame masa babban dalilin dawowa a cikin mu, domin mu kara yi wa al’umma gudummawa mai dimbin yawa.
“Idan ana samun mutane nagari irin su Umahi, to dimokradiyya za ta kara nagarta, inganci da kwarjini.
Yayin da ake ta maganar komawar Umahi na Jihar Ebonyi APC, a gefe daya kuma ‘yan PDPin Ebonyi da ke Majalisar Tarayya ba za su bi Gwamna Umahi zuwa APC ba.
Kungiyar ‘Yan Majalisar Dattawa da ta Tarayya na PDP daga Jihar Ebonyi, sun bayyana cewa ba za su bi Gwamnan Ebonyi Umahi cikin jam’iyyar APC ba.
Shugaban su Sanata Sam Egwu tare da sauran sanatocin jihar da Mambobin Majalisar Tarayya biyar ne su ka bayyana haka, a matsayin martanin su, bayan Gwamna David Umahi ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Sanata Egwu, wanda ya yi bayani a madadin sauran baki daya, ya ce: “Bari na kawar da tunani ko shakku, na warware magana a zahiri da badini. Babu wani Sanata ko Dan Majalisar Tarayya guda daya rak da zai bar PDP ya koma APC.
“Mu sanatoci uku da Mambobin Tarayya su biyar, duk mu na nan a PDP, kuma har yau har gobe babu wanda ke shawa’ar barin PDP, jam’iyyar mu da mu ke kishi da kauna.
Sun ce dalilin ficewar Umahi daga PDP na can an rigaya an watsa, duniya ta gani. Ya ce saboda PDP ba ta yi wa yankin Kudu maso Gabas adalci ba, wajen fitar da dan takarar shugaban kasa da kuma mataimakin shugaban kasa.
Egwu ya ce duk da su din ma su na goyon bayan a bai wa dan yankin kabilar Igbo takarar shugabanci, to amma gaskiya ba su goyon bayan ficewa daga PDP.
“Ficewa daga jam’iyya rashin mutunci ne, rashin dabara ce, ba halin kirki ba ne ga tafiyar siyasa. Sannan kuma rashin tunani ne ka bada sharudda ko wa’adin tilas sai an ba ku takara.
“Idan ma akwai wanda zai fi yi kowa gode wa PDP, ai David Umahi ne. Mutumin da aka dora shugaban jam’iyya. Daga nan aka tsaida shi takarar gwamna, har ya yi nasara sau biyu, duk a karkashin PDP.
Egwu ya bada labarin yadda aka dauko ‘yan uwan gwamnan aka ba su manyan mukamai.
Bayan ficewar sa daga PDP, Umahi ya zargi Gwamna Wike na Ribas da yin kane-kane a PDP, ya maida kamar shi ne ke da jam’iyyar.
Sai dai shi kuma Wike ya maida kakkausan raddin cewa magagin barci ne ke dibar Umahi, inda ya ke mafarkin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin APC.