Likita Azubuike Iheanacho da masu garkuwa su ka damke, a Karamar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi, ya bayyana cewa sai da ya biya maƙudan kuɗaɗe kafin ƴan bindigar da su ka damke shi su ka sake shi.
Iheanacho, wanda ke da asibitin Peace Hospital, kuma mamba na Kungiyar Likitocin Jihar Kogi, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa sai da ya wale wa masu garkuwa naira milyan 3 tukunna, kafin su sake shi.
“Gaskiya na ji ciwo, amma dai raunin ba mai yawa sosai ba. Saboda da farko kin yarda na yi su tafi da ni. Kuma a kan idanun jama’a su na gani aka tafi da ni babu yadda za su yi. Amma ina kara godiya ga Ubangiji, tunda na kubuta.
Ihreanacho ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro su tashi tsaye wajen kare rayukan jama’a, kasancewa garkuwa da mutane ta yi matukar muni sosai a kasar nan.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Kogi, Williams Aya, bai ce komai a kan batun ba. Duk da ya ce zai waiwayi wakilin mu domin yi masa karin bayani, har yanzu lokacin rubuta wannan labari bai kira ba.
A cikin makon da ya gabata, an yi garkuwa da mutum tara, wadanda kafafen yada labarai su ke da sahihin labarin kama su da aka yi.
Sai dai kuma babu tabbacin ko mutum nawa aka yi garkuwa da su yayin da mahara su ka kai hari a wani masallaci a jihar Zamfara.
Cikin wadanda aka yi garkuwa da su a makon da ya gabata, har da Tofai Nanono, dan uwan Ministan Harkokin noma, Sabo Nanono, wanda aka yi garkuwa da shi a kauyen su da ke cikin Karamar Hukumar Gabasawa, a jihar Kano.
Idan ba a manta ba, a cikin makon me Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa lalacewar garkuwa da mutane ta kai jama’a na ajiye abinci a gida, saboda gudun kada masu garkuwa su shiga gidajen su, su nemi kayan abinci su rasa.