Na dade ina ta rattaba lissafe-lissafe, yadda abubuwa da zasu kasance ace wai matasan Arewa ne suka tattago zanga-zanga irin na #EndSARS a Kasar da abin ya fi kazanta a lokacin da akalar ta tsinke.
An rika yadawa a shoshiyal Midiya cewa da dama daga cikin manyan Arewa sun yi maza-maza sun garzaya wajen malamai da manyan gari, sun nemi su taya su tausa matasan Arewa kada su biye wa zanga-zangar #EndSARS, duk da ko matasan dama can basu da niyyar biye wa wadanda suka shirya wannan zanga-zanga.
Basu yarda da manufar masu zanga-zangar ba tun farko wanda a dalilin haka ma kiraye-kirayen yayi tasiri.
Sai dai kuma a kwana a tashi, idan ba gaggauta daukan mataki akayi ba wajen bijiro wa matasan tsare-tsare da zai taimake su wajen gyara musu tarbiya da samar musu da sana’o’i da ilimi ba, zan ce tana kasa ta dabo kenan.
Domin sai dai mu yi ta samun mulki amma ba bu abinda ake tabuka wa yankin da mutanen ta.
Wani abin yabawa da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ke yi shine kokarin hada kan shugabannin yankin musamman gwamnonin yankin su zo a rika zama ana tsara hanyoyin da za abi don gyara yankin da mutanen ta.
An yi ta yin ganawa a tsakanin gwamnoni da sarakunan yankin domin aga yadda za a shawo kan matsalolin da ake fama dasu.
Babbar matsalar da ya addabi Yankin Arewa
Matsala daya da ta zamo wa yankin Arewa yanzu kashi a wuya shine matsalar Garkuwa da mutane da tilasta wa ƴan uwa su tara kudin da basu ji ba basu gani ba, su mika wa wadansu mahara haka kawai don a saki dan uwansu da aka kama.
Matsalar garkuwa da mutane ya faro ne kamar da wasa, tun ana ganin shi sabo, yanzu ya kai ga da alamar ya ma fi karfin gwamnatocin jihohin yankin da ƙasar ne zan ce ko kuma ƙaƙa ake ciki?
Babu inda ba a sace mutane ya yankin yanzu, saidai jihohin Kaduna, Katsina, Jigawa, Zamfara, sun zama hedikwatar masu sace mutane. Kusan kullum sai ka gani a kafafen yada labarai wai an sace wani ko wata kuma ana ƙoƙarin a biya kuydin fansa.
Abin tambaya shine, gabaɗaya shugabannin tsaron kasar nan kaf din su ƴan Arewa ne, yau da ƴan kudu ne da abinda da za a rika cewa da ban. Gashi shugaban kasa daga Arewa yake, idan abin ya gagara ne duk da mu da su sai mu koma mu ware wasu kwanaki na musamman, A yi azumi ayi ta salati ga Annabin Tsira SAW da istigfari a yi tawassali da su a roki Allah ya kau mana wannan masifa, yanzu kam hakan shine kawai nake gani mafita.
Mata masu ciki basu tsira ba, yara basu tsira ba, talaka bai tsira ba, mai kudin ma bai tsira ba.
Allah nake roko, ya kawo wa yankin mu zaman Lafiya da kuma karshen wadannan masifu da muke fama da su a yankin Arewa da kasa baki daya.