Sabuwar cuta ta kashe mutum 17, wasu na kwance a asibiti a jihar Benuwai

0

A ranar Talata Jaridar ‘Daily Post’ ta buga labarin cewa wata cuta da ba a san irinta ba ta kashe mutum 17 sannan Wasu da dama na kwance a asibiti a jihar Benue.

Cutar ta bullo a kauyen Okpeilo-Otukpa dake karamar hukumar Ogbadibo.

Babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Sir Andrew Amee ya tabbatar da haka yana mai cewa akwai mutum daya dake dauke da irin wannan cuta ya na kwance a asibitin koyarwa na jami’ar Benue dake Makurdi.

Alamun kamuwa da wannan cuta sun hada da zazzabi, ciwon ciki, amai da bahaya da jini.

Amee ya ce gwamnati ta ware isassun kudade masu yawa domin ma’aikatar kiwon lafiya ta yi binciken gano ko wacce irin cuta ce da kuma maganinta.

Gwamnati ta yi kira ga mutane da su tsaftace muhallin su domin gujewa kamuwa da cututtuka.

PREMIUMTIMES ta buga labarin yadda jihohin Enugu da Delta suka sanar wa Hukumar NCDC bullowar wata cuta da ba a san irin ta ba a jihohinsu.

Rahoton ya nuna cewa jihar Enugu ta rasa mutun sama da 50 sannan 22 a jihar Delta a dalilin cutar.

Bayan hukumar NCDC ta gudanar da bincike sakamakon ya nuna cewa cutar shawara ce ta buwayi mutane a wadannan jihohi.

WHO, NPHCDA da ma’aikatar kiwon lafiya sun hada hannu domin dakile yaduwar cutar.

An kuma samu labarin bullowar cutar shawara a jihar Bauchi inda ta yi ajalin mutum 8 a jihar a ranar Litini.

Share.

game da Author