Gwamnatin tarayya ta ce zanga-zangar da matasa suka yi na #EndSARS na daga cikin dalilan da ya sa abinci ya yi dan karan tsada a kasar nan.
A cewar gwamnati, a dalilin wannan zanga-zanga ba a samu damar yin safara da jigilar abinci da sassan kasar nan ba saboda yamutsi da ya tirnike a dalilin wannan zanga-zanga da sannan kuma saka dokar hana walwala da gwamnatoci suka sassaka.
Kakakin mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, Laolu Akande ya Sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai.
Sauran matsalolin dake da nassaba da tashin gwauron zabi da kayan abinci suka yi sun hada da hare-haren mahara da ya addabi mutanen yankin Arewa maso Yamma, annobar Korona, Karin kudin mota da aka yi da rikicin makiyaya da manoma.
A cikin ‘yan kwanakin nan farashin kayan abinci sun tashi sun yi tashin gwauron zabi.
A yanzu haka buhun shikafa kg 50 da ake siyar da shi Naira 26,000 ya tashi zuwa 32,000.
A watan Janairu 2020 ana siyar da buhun albasa 20,000 yanzu wannan buhu na albasa ta harba zuwa 80,000.
Buhun garin kwaki ya kara kudi zuwa sama da Naira 24,000 din a aka sani a da.
Bayan haka rahotan tsadan farashin abinci da hukumar NBS ta fitar a watan Yuli ya kai kashi 15.48%
Daga nan dai ya karu zuwa kashi 16.0% a watan Agusta sannan ya kai kashi 16.66% a Satumba.