RASHIN TSARO: Ƴan bindiga sun kashe mutum 11 a Albasu, kauyen Igabi, Jihar Kaduna

0

A ranar Litinin ‘yan bindiga su ka kai hari a kauyen Albasu da ke cikin Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna. Sun kashe mutum 11su ka raunata mutum hudu.

Wani manomi da ke kusa da kauyen mai suna Musa, ya bayyana cewa ya ga wucewar ƴan bindigar a kan babura da rana tsaka kafin Sallar Azahar.

“Ina cikin gona ta kusa da kauyen sai na rika jin rugugin harbe-harben bindiga. Daga nan kuma sai na ga ana ta fito da mutanen da aka ji wa ciwo jinajina.

“Daga baya an ce an kashe mutum 11. Dama kuma an dade ‘yan bindigar na kokarin shiga kauyen, amma abin ya na gagarar su. Sai wannan karo su ka ci karfin garin.

Sun kai harin lokacin da yawancin mazan kauyen su na gona.

Shi kuma dagacin Albasu mai suna Nuhu Abubakar, ya ce ‘yan sanda sun je kauyen, bayan maharan sun rigaya sun yi kisan sun tafi.

“Mun yi wa gawarwakin da aka kashe sallah. Amma bayan kisan, maharan sun tafi da shanun jama’a.”

Ya ce yanzu zuwa gonakin su ya gagare su saboda tsoron masu garkuwa da jama’a. Ya yi kira ga gwamnati ta kare rayuka da sukiyoyin su.

Gwamnatin jihar Kaduna ta hannun Kwamishinan Tsaro, Samuel Aruwan, ta tabbatar da kisan mutanen 11.

Wadanda ‘yan bindiga su ka kashe sun hada da Amadu Malam, Idi Gefefe, Isa Goma, Awwalu Goma, Babangida Iliyasu sai Lado Iliyasu.

Sauran sun hada da Ya’u Jumare, Hamza Umaru, Shehu Jibrin, Tukur Albasu da Musa Adamu Muruzuwa.

Share.

game da Author