Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa, ya ragargaji yadda Gwamnatin Buhari ta kyale jihohi irin su Zamfara su na cin moriyar kudaden gwala-gwalan da ake hakowa a jihar su su kadai, amma kuma aka hana Jihohin Yankin Neja-Delta su rika cin moriyar arzikin danyen man fetur da gas din su.
Da ya ke magana ranar Laraba, Gwamna Okowa ya ce wannan nuna bambanci ne, kuma rashin adalci ne. Okowa ya ce dukkan jihohin yankin Kudu-maso-Kudu, sun hadu a kan goyon bayan sake fasalin kasar nan.
Jihohin da su ka kunshi kudu maso kudu, sun kunshi Delta, Rivers, Bayelsa, Cross River da sauran su.
Gwamnan ya yi bayanin a taron sa ya ke ganawa da manema labarai duk bayan watanni uku a Asaba, babban birnin jihar Delta.
Ya ce akwai bukatar sake fasalin Najeriya, domin a kara wa jihohi wasu iko su da kananan hukumomi.
Okowa, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Kudu maso Kudu, ya ce Najeriya ta kasa ci gaba, saboda an hana jihohi cin gashin albarkatun arzikin da ke yankunan su.
Ya ce batun kyale jihohi su yi iko da albarkatun kasa da ke jihohin su, sake fasalin Najeriya da kuma tsaro, su ne barutuwan da gwamnonin kudu maso kudu za su fi maida hankali, idan tawagar Shugaban Kasa ta kawo ziyara domin tattaunawa da Shugabannin Yankin Kudu maso Kudu.
Za a dai yi wannan gagarimin taro ranar Juma’a mai zuwa a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Da ya ke magana a kan yadda aka kyale Zamfara na cin gashin gwalagwalan sa ake hakowa a jihar kuwa, Gwamna Okowa cewa ya yi, akwai Doka ta Majalisar Tarayya wadda ta yi magana a kan albarkatun danyen mai da gas da kuma sauran albarkatun cikin gida na karkashin kasa.
“Ba zai yiwu ka rika amfani da doka a yankin Neja Delta ba, a hana mu damar amfanar albarkatun cikin kasar mu, ita kuma Zamfara a kyale ta na tatsar na ta gwala-gwalai ita kadai. Sannan kuma a raba na mu kudin tare da Zamfara.”
Dokar Najeriya dai ta ce duk wasu albarkarun cikin kasa da na ruwan Najeriya, to mallakar Gwamnatin Najeriya ne.
Sai dai kuma wasu da dama na ganin cewa kamata ya yi jihohi su rika hako albarkatun cikin jihohin, amma su rika ba Gwamnatin Najeriya haraji.
Haka kuma jama’a sa dama na sukar yadda wasu gwamnonin Arewa ke sa ana kama kwalaben giya ana fasawa, amma kuma a gefe daya, ana ba su kason kudade daga harajin kudaden cinikin giya.
Discussion about this post