RAMCE DAGA BRAZIL: Abubuwa 10 Da Gwamnatin Buhari Za Ta Yi Da Bashin Kayan Noma Na Dala Bilyan 1.2

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana abubuwan da za ta yi da bashin dala bilyan 1.2 wadanda za ta ciwo daga kasar Brazil, idan Majalisar Dattawa ta amince.

A farkon makon da ya gabata ne Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ta bayyana wa Majalisar Dattawa bukatar ciwo bashin domin shirin bunkasa harkokin noma na tsawon shekaru goma.

Bashin na dala bilyan 1.2 da za a ciwo daga kasar Brazil, adadin kudaden na daidai da naira bilyan 459.

Sanatoci da dama sun nuna damuwa da yadda Najeriya ke fita waje ciwo bashi ido-rufe.

Minista Zainab ta fada wa Sanatocin cewa a yanzu tulin bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 31.01.

Ta ce amma nan da karshen shekarar 2021, bashin zai kai naira tiriliyan 38.68, saboda Najeriya za ta ciwo karin naira tiriliyan 4. 78 domin cike gibin Kasafin 2021.

Tun cikin watan Yuni, lokacin da Ministan Harkokin Noma Sabo Nanono ya yi taro da manema labarai, tare da Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, Lai ya yi karin bayanin yadda za a kashe lamunin na naira bilyan 459 kamar haka:

1. Gwamnatin Tarayya za ta tanaji filin noma mai fadin hekta 100,000 a kowace jiha.

2. Za a yi aikin gina kananan titina zuwa lungunan da filayen noman su ke, domin saukake zirga-zirgar aikin goma da kuma rika kwasar amfanin gona zuwa kasuwanni.

3. Wannan shiri ne da zai dauki shekaru 10 ana gudanar da shi. Daga nan kuma zai zarce sadidan bayan ya zama game-gari.

4. Bankin Development Bank na Brazil da Deutsch Bank ne za su bada ramcen kudaden.

5. Kamfanin Inshora na Brazil da Kamfanin Inshora na Bankin Musulunci na Duniya ne za su tsaya wa Najeriya bisa bada inshora, ko da reshe zai nemi juyewa da mujiya.

6. Za a rika sayo bangarorin jikin taraktar noma (spare parts) daga Brazil ana harhadawa a nan Najeriya. Akalla duk shekara za a hada taraktar noma 5,000 har tsawon shekaru 10 a jere.

7. Za a kafa Cibiyoyin Casa, Tankade da Rairaye Kayan Gona har guda 142. A kowace Shiyyar Sanata za a kafa guda daya.

8. Za a gina wuraren ajiya da gyaran taraktocin noma a kowace karamar hukuma, har guda 774.

9. Shirin mai suna ‘GREEN IMPERATIVE’, zai samar da aiki ga matasa sama da milyan 5.

10. Zai bunkasa damar samun abinci mai gina jiki ga mutum milyan 35, tare da bunkasa tattalin arzikin wasu mutum sama da milyan 35.

Share.

game da Author