Ma’aikatar Jinkai da Agaji ta karbi naira bilyan 258.4 tsakanin Janairu zuwa Satumba 2020. Amma daga cikin kudin ta kashe naira bilyan 96.3, a cikin watanni tara din.
Wannan ya na cikin wasu takardun bayanan da ma’aikatar ta aika Majalisar Tarayya ga Kwamitin Yaki da Fatara da Talauci.
Kashi 99 na kudaden da aka kashe din daga naira bilyan 96, an kashe su ne wajen Shirin Tallafa Wa Marasa Galihu. Wato a karkashin shirin, an kashe naira bilyan 95.2 kenan.
Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu, wato NSIP kenan wanda aka kashe kudaden a karkashin sa, takardun bayanai sun nuna cewa naira bilyan 66.1 aka kashe wajen shirye-shiryen yau da kullum. Sai kuma naira bilyan 29.1 a manyan ayyuka.
Shirye-shiryen NSIP sun hada da N-Power da ake daukar masu digirin da ba su da aikin yi, shirin GEEP, Tsarin Tura Wa Marasa Galihu Kudi a Asusun Banki (CCT), sai shirin ciyar da yara ‘yan makaranta.
An tsara za a kashe naira bilyan 374.4 a shirin NSIP, bayan an yi wa kasafin 2020 kwaskwarima saboda matsalar kudi da gwamnati ta fuskanta, sanadiyyar barkewar cutar korona.
Akwai naira bilyan 32.5 daga cikin kudaden, wadanda aka ware ga shirin tura wa marasa galihu su milyan 1 kudade a asusun su na banki, sai kuma mutanen da aka rika tura wa naira 5,000.
Takardun bayanan sun nuna cewa an sakar wa ma’aikatar naira bilyan 256 daga cikin naira bilyan 374.4.
“Sai dai kuma har yau ma’aikatar ba ta kai ga karbar kudaden Shirin Tura wa Marasa Galihu Kudaden Rage Radadin Korona ba.” Haka takardun bayanan su ka nuna.
Ma’aikatar ta kuma yi bayanin dalilin da ya sa har yau ba ta aiwatar da sama da kashi 50 na aikin kudaden shirye-shiryen NSIP ba.
“Barkewar cutar korona ce ta sa ba mu samu damar aiwatar da sauran ayyukan ba.” Haka ma’aikatar ta bayyana a cikin kwafen takardun bayanan, wadanda ta tura wa ‘Yan Majalisa a cikin Oktoba.
“Amma ayyukan kwangilolin da ke karkashin manyan ayyuka su duk sun yi nisa matuka.” Inji bayanan da ke cikin takardun.
Jimillar abinda aka tsara ma’aikatar za ta kashe a kasafin 2020 naira bilyan 378.8 ne. Ya zuwa Satumba, an sakar mata naira bilyan 258.4, anma a cikin kudin naira bilyan 96.3 kadai aka samu sararin kashewa aka yi ayyuka da su. Haka dai takardun bayanan su ka nuna.
Sauran Canjin Naira Bilyan 162.1:
Wannan ya nuna Ma’aikatar Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa na sa sauran kudi naira bilyan 162.1 ajiye a asusun ta, wadanda ba ta yi ayyuka da su ba a karkashin kasafin 2020, saboda dalilin tsayawar komai a dogon lokacin da aka dauka zaman dakile cutar korona.
Hakan na kunshe cikin rahoton da ma’aikatar ta damka wa ‘yan majalisa a cikin Oktoba.