RAHAMA SADAU: Mansurah Isah ta caccaki ƴan Kannywood, Hafsat Shehu ta maida mata da martani

0

A cigaba da tofa albarkacin baki da mutane ke yi kan yadda wani ya yi wa Annabi, SAW izgilanci a shafin jaruma Rahama Sadau na Tiwita, da ita kanta jarumar abin dai yauki wani sabon salo.

Mansurah Isah wanda uwargidan jarumi Sani Danja ce ta caccaki masu yi wa Rahama Sadau ruwan tsinuwa a shafukan su na sada zumunta a yanar gizo cewa duk kanwar fa ja ce.

Tashar Tsakargida dake yada labaran ta a Youtube ne ta ruwaito yadda tsoffin jaruman biyu suka rika tona wa juna asiri a shafukan yanar gizo.

Mansurah dai ta ragargaji musamman mata masu nuna rashin jindasu kan hotunan da Rahama ta saka a shafinta ta Tiwita da ya kawo cece-kuce, har ya kai ga an yi wa musulunci izgilanci cewa suma masu wage baki ba sal-sal suke ba.

Kamar yadda tashar ta ruwaito, mansurah ta zarge su da cewa suma masu wage bakin ba mutanen arziki bane, sannan ta kalubalanci mutane da su garzaya shafukan su suga irin hotunan da suke sakawa, cewa duk kanwar ja ce.

Sai dai ba da dadewa da ta saka wannan kalamai ba abokiyar aikin ta a baya, wato Hafsat Shehu, ta maida mata da martani cewa ta ja bakinta ta yi wa mutane shiru domin ita ma din akwai alamar tambaya a al’a muranta.

Sai dai kuma Rahama ta bayyana wa BBC Hausa cewa ita ce abin tausayi ba wasu ba domin an saka kalaman batancin a shafinta ne a dalilin hoton da ta saka.

” Ko da aka sanar da ni cewa wani yayi wannan kalamai, na gaggauta cire hotunan. Duk da cewa mutane duk sun dauka. Na yi matukar yin nadama.

Share.

game da Author