Kamfanin Pfizer dake kasar Amurka da Kamfanin BioNTech dake kasar Jamus sun hada maganin rigakafin kamuwa da kwayoyin cutar korona dake da aka tabbatar da ingancin sa da akalla kashi 90 bisa 100.
Wadannan Kamfanonin sun hada wannan magani ƙasa da lokacin da ake zaton za a kammala hada shi kuma har sun yi gwajin ingancin sa a jikin mutane sama da 44,000.
Kamfanonin na sa ran cewa gwajin ingancin maganin da ake yi ba zai dauki tsawon lokaci ba domin samun izinin fara amfani da maganin.
Hada maganin cutar korona
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ce kungiyar dake kula da ingancin magungunan da masana kimiya a fadin duniya ke kokarin hadawa.
Bisa ga ka’ida hada maganin zai dauki tsawon shekara daya da wata shida ne.
Kungiyar na sa ran samun biliyoyin ruwan maganin nan da shekara 2021 domin raba wa kasashen duniya.
Zuwa yanzu akwai Kamfanonin 150 dake himman suma su hada maganin korona a duniya, sai dai kuma da kyar za a samu guda daya dake da ingancin kawar da cutar a wanna shekara.
Burin WHO shine samar da maganin dake da ingancin kashe kwayoyin cutar korona ba tare da ya cutar da kiwon lafiyar mutane ba.
Yaduwar cutar korona
Cutar korona ta yadu zuwa sama da kasashen 200 a duniya.
Mutum sama da miliyan 50 sun kamu da cutar a duniya sannan sama da miliyan 1.2 sun mutu.
A Nahiyar Afrika cutar ta yadu zuwa kasashen 54 inda mutum 1,506,185 sun kamu da cutar sannan mutum 36,000 sun mutu.
Mutum 1,127,034 sun warke a Afrika.
A Najeriya mutum 64,090 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 59,910 sun warke, 1,154 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,026 ke dauke da cutar a Najeriya.