PDP ta ci amanar Inyamirai, shi yasa na koma APC, ta fi gwabi-gwabi – Gwamna Umahi

0

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta yaudari ƴan kabilar Igbo a kasar da nuna musu kiyayya karara na kin ba dan yankin damar yin takarar shugaban kasa ba.

An dade ana ta raderadin cewa akwai yiwuwar gwamnan na Ebonyi, Umahi ya fice daga PDP ba tun yanzu ba.

Wannan kwai da ya fasa ya kawo karshen haka.

Umahi ya ce, sai dai ace yau wancan ne gobe a ce wannan, babu wata dama da jam’iyyar ta basu duk da goyon baya da take ba jam’iyyar 100 bisa 100.

” Tun 1999 ake ta gafara ga shanu nan amma haryan zu ko sawun sa ba mu gani ba. Bayan irin rungumar gani kashe ni da muka yi wa jam’iyyar PDP a kasar nan. Wannan shine babban dalilin da yasa na ga ba zan cigaba da biye wa yaudarar PDP ba da ni da sauran ƴan uwana Inyamirai.

” Bayan haka ina so in fede muku biri saga kai har wutsiya kusani cewa, ban taba neman kujerar shugaban kasa ba ko kuma wai PDP ta tsaida ni dan takara. Musu wannan magana su sani ba a taba haka ba. Idan ma haka ne ai deliget akalla 8000 ne za su yi zabe ba ni zan zabi kai na ba.

” Tsakani da Allah abin kunya ne da cin fuska ace wai tun daga 1999 PDP ba zata iya tsaida dan kabilar Igbo yayi takarar shugaban kasa ba duk da irin goyon bayan da yankin ta rika ba jam’iyyar.

Umahi ya kuma karyata masu cewa wai anyi masa alkawarin wata kujera ce a APC cewa ba bu magana mai kamar haka tsakanin sa da APC, ya ce shi dai yafi gani kila APC ta fi yi wa Inyamirai adalci a nan gaba fiye da PDP da yankin tayi ta bauta mata fiye da shekaru 20.

Share.

game da Author