Kamfanin NNPC ya bayyana farashin litar fetur daga daffo-daffo na rumbunan ajiyar fetur, cewa za a rika sayar wa masu gidajen mai a kan naira 153.17 a watan Nuwamba.
Kakakin NNPC Kennie Obateru ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a Abuja cewa wannan farashin watan Nuwamba ne.
Shi dai farashin da ake saida wa dillalai, ba daidai ya ke da farashin da masu mota ke sayen lita a gidajen mai ba.
Idan dillalai su ka sayo a daffo, za su dora riba, gwargwadon yadda Hukumar Kayyade Farashin Litar Fetur da Gas ta kayyade.
A baya, masu gidajen mai ba su dora riba, sai dai gwamnatin tarayya rika ba su tallafi, daidai nisan ka da daffo din da ka sayo mai.
Idan mai gidan mai na garin Ibadan ya sayo fetur a daffo din Lagos, to tallafin da gwamnati za ta ba shi ba zai kai na mai gidan mai da ya dauka daga Lagos zuwa Katsina ko Jigawa ba.
Kenneth ya shawarci dillalan fetur su sayi man su kai-tsaye ta ‘online’, a manhajar intanet na shafin: (PPMCCustomer.Express/login/authenticate) a kan farashin da aka bayyana a sama.
Ya ce ba gsskiya ba ne da aka rika watsa bayanai da labarai cewa naira 155.17 kudin lita daga daffo a farashin sayar wa dillalan fetur.