NEXIT: Najeriya ta buɗe shafi domin sake ɗaukar matasan N-Power ɗin da aka sallama

0

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon shafin yanar gizo na ‘portal’mai suna NEXIT, domin sake daukar matasan da ke cin gajiyar Shirin Inganta Rayuwar Al’umma na NSIP, wadanda aka sallama daga aikin N-Power.

Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq ta ce an bude shafin na NEXIT ne tare da hadin guiwar Babban Bnakin Najeriya, CBN, domin wadanda za su ci moriyar shirin su samu damar cika fam kai-tsaye a bangarorin ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban.

Kakakin Yada Labarai na Ma’aikatar Jinkai da Agaji, Nneka Anibeze ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a.

Minista Sadiya ta ce tashar ta ‘portal’ din mai suna NEXIT ita ce za ta buba cancantar wurin da ya fi dacewa a tura duk wanda zai ci moriyar shirin.

Ta kara da cewa CBN ne zai gindiya sharuddan da za a cika kafin mutum ya camcanta a dauke shi.

Daga nan sai Sadiya ta yi kira ga duk wanda maciya gajiyar N-Power da aka sallama a baya su gaggauta shiga shafin NEXIT a intanet su sake cikawa domin sake cin gajiyar wannan shiri a karkashin bankin CBN.

Daga nan ta gode wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile bisa kokarin da ya key i wajen bada goyon baya ga shirin. Ta na mai karawa da cewa ma’aikatar ta na a sahun gaba wajen tabbatar da kuridin Shugaba Muhammadu Buhari na fitar da mutane milyan 100 cikin kangin fatara da talauci a cikin shekaru 10 ya tabbata.

Share.

game da Author