Namadi Sambo ya yi kira ga gwamnati ta rika tallafawa jami’o’i masu zaman kansu a kasar nan

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya yi kira ga gwamnati ta rika taimaka wa jami’o’i masu zaman kansu da tallafin kudade domin ayyukan gudanarwar jami’o’in.

Sambo ya yi wannan roko ne da yake jawabi a wajen taron kungiyar tsofaffin daliban jami’o’in Najeriya (CAANU) wanda aka ranar Asabar a Kaduna.

Tallafa wa jami’o’i masu zaman kansu da kudade zai basu damar zurfafa bincike a fannonin fasaha da Kimiyya da kuma kara musu karfin guiwa wajen maida hankali ga karatun dalibai a jami’o’in.

Ya yi kira da a kafa asusun bayar da tallafi ga jami’o’i wanda mambobin kungiyar tsofaffin daliban kowace jami’a za su tafiyar da su da kula da su domin cigaban ilimi da jami’o’in.

Ya ce gwamnati kadai ba za ta iya kula da jami’o’in kasar nan ba, dole sai an sa mata hannu ta hanyar hada karfi da karfe domin a iya kaiwa ga nasara.

Tsohon mataimakin shugaban kasan, shine Cansalan jami’ar Baze dake Abuja.

Share.

game da Author