Manajan Shirin kawar da cutar dundumi ‘ River blindness’ na ma’aikatar kiwon lafiya Michael Igbe ya ce mutum miliyan 50 na cikin hadadrin kamuwa da cutar dundumi a Najeriya.
Igbe ya fadi haka ne a taron musayar ra’ayi kan yadda za a kawar da cutar a sashen kare yara kanana na ma’aikatar yada labarai da asusun bada da tallafi ga kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF suka shirya.
Akan kamu da cutar dundumi wanda ke sa makanta idan kudan da ke dauke da tsutsa a jikin sa da ake kira ‘Blackfly’ ya ciji mutu sai ya saka masa dafin wannan tsutsa a jikin sa.
Ba a gane alamun cutar da wuri a jikin mutum sai bayan tsutsan ya dade kamar tsawon shekara daya.
Bayan haka ne alamu kamar kuraje da makanta ke bayyana.
A bayanin da ya yi Igbe ya kara da cewa cutar na ci gaba da yaduwa a Najeriya a dalilin rashin maida hankali wajen daukan matakan kawar da cutar da gwamnati bata yi ba.
Ya ce gwamnati ta fara amfani da maganin ‘ivermectin’ a shekarun 1989 da 1997 a duk jihohin kasar nan domin kawar da cutar.
Igbe ya ce ya zama dole gwamnati ta farga tun da wuri ta ware isassun kudade domin kawar da cutar domin kare mutanen kasar nan.
Sanna kuma da wayar wa mutane kai game da hadarin da ke tattare da kamuwa da cutar da kuma yadda za a iya kauce wa kamuwa da ita.
Discussion about this post