Mutum biyar masu garkuwa suka sace, biyu sun mutu a titin Abuja-Kaduna ranar Lahadi

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa an yi garkuwa da mutum biyar a titin Abuja zuwa Kaduna ranar Lahadi.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ya fadi haka a wani takarda da ya raba wa manema labarai a garin Kaduna ranar Litini.

Aruwan ya ce gwamnati ta Samu labarin adadin yawan mutanen da aka yi garkuwa da su daga bakin ƴan uwan wadanda aka yi garkuwa da su.

Ya ce gwamnati ta aika da bayanan haka ga jami’an tsaro domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su sannan da kamo masu garkuwan.

Bayan haka Aruwan ya tabbatar cewa mutum biyu ne suka mutu ranar Lahadi ba mutum 12 da aka rika yadawa ba.

” Mahukuntan Asibitin Doka, sojoji, jami’an ƴan sandan, da na hukumar kiyaye hadurra, FRSC sun tabbatar cewa mutum biyu ne suka mutu.

Sannan kuma Aruwan ya karyata jita-jitan da ake yadawa cewa babu jami’an tsaron dake yin sintiri a titin Abuja – Kaduna, yana mai cewa an sassaka jami’an tsaro a muhimman wurare a hanyar domin kariya ga matafiya.

Sannan kuma ya ce duk da garkuwa da mutane tara din da aka yi a ranar Lahadi gwamnati ba za ta karaya ba wajen kare mutane a hanyar.

A labaran PREMIUM TIMES HAUSA na yammacin litini, gwamnatin Kaduna ta bayyana yadda dakarun tsaro suka fatattaki mahara a titin sannan suka ceto wasu da aka yi garkuwa da su har mutum 9.

Share.

game da Author