Ƙungiyar Kare Muradun Musulmin Najeriya (MURIC), ta ja hankalin ‘yan Najeriya, musamman Musulmi su guji jefa kan su cikin wata sabuwar zanga-zangar #EndSARS da ake kishin-kishin din sake tadawa.
Shugaban MURIC Ishaq Akinbola ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce MURIC ba ta goyon baya, kuma ta na bai wa ‘yan Najeriya musamman Musulmai shawara kada su shiga zanga-zangar kwata-kwata.
“Kowa ya shaida irin kazami kuma mummunan barnar da ta biyo bayan zanga-zangar #EndSARS da aka yi. Saboda haka ba mu goyon bayan sake tada wata tarzoma a kasar nan.
“Doka ta amince zanga-zanga halas ce, amma idan ta lumana ce. Amma muddin ta rikide zuwa tarzoma, to wannan tabbas an take doka, an kuma wuce iyaka.
“Tunda har gwamnatin tarayya ta amince za ta cika sharudda biyar da masu zanga-zanga su ka gindaya, to kamata ya yi sai a hakura, kowa ya jira, ya ga abinda gwamnati za ta yi.
“Akwai tantiran ‘yan iska da tantagaryar masu aikata muggan laifuka da ke son ganin bayan jami’an tsaro. Irin wadannan su na son tayar da tarzoma. Don haka mu ke cewa duk mutumin kirki, nagari mai bin doka da oda, to ya kiyayi sake tada wata sabuwar zanga-zanga.”
PEWMIUM TIMES ta buga labarin yadda Gwamnatin Najeriya ta yi wa kudaden masu zanga-zanga kamun-kazar-kuku a bankuna.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Babban Bankin Najeriya (CBN) iznin kulle asusun ajiyar wasu jagororin zanga-zangar da ke bankuna daban-daban.
Babban Bankin Najeriya ne ya nemi Mai Shari’a Mohammed Ahmed ya ba shi iznin kulle asusun bankunan na su, tun a ranar 20 Ga Oktoba.
PREMIUM TIMES ta ga wasikar da kotu ta tura wa Access Bank, Fedility Bank, First Bank, Guaranty Trust Bank, UBA da kuma Zenith Bank, inda aka umarce su kada su sake su bar masu asusun ajiyar a bankunan na su har su 20 su taba ko sisi cikin kudaden ajiyar na su.
Umarnin ya nuna cewa gwamnati na so ta yi amfani da kudaden da ke cikin asusun su a matsayin shaida.
Dalili kenan aka ce kada a bari su 20 din su taba kudaden ajiyar ta su, har sai bayan kwanaki 180, yadda kafin lokacin an kammala duk wani binciken da ya kamata a yi a kan su.
Wasu ‘yan gaba-dai-gaba-dai din #EndSARS da abin ya shafa sun hada da Bolatito Racheal Oduala, Chima David Ibe, Mary Doose Kpengwa, Saadat Temitope Bibi, Bassey Obi, Nicholas Ikhalea Osazele, Ebere Idibie, Akintomide Lanre Yusuf, Uhio Ezenwanyi Promise da Mosopefoluws Odesepe.
Sauran sun hada da Adegoke Pamilerin Yusuf, Umoh Grace Ekanem, Babatunde Vicror Segun, Mulu Louis Teghenan, Mary Oshifonawora, Winifred Akpevweoghene Jacob, Victor Solomon, Idunu Williams da Gatefield Nigeria Limited.
Duk da gwamnati ta amince za ta cika dukkan sharuddan da masu zanga-zangar su ka nema, sai kuma ga shi yanzu ta koma kokarin bin wasu da su ka hada zanga-zangar da kokarin yi masu bi-ta-da-kulli.
A farkon makon nan ne aka hana wata lauya wadda ta na cikin #EndSARS fita Turai, kuma aka kwace fasfo din ta.