Ministar Harkokin Kudin Kasa, Zainab Ahmed ta kalubalanci iyaye, shugabannin Al’umma da sarakuna da su maida hankali wajen baiwa ƴaƴansu tarbiya na nagari kamar yadda suma iyayen su suka basu a da.
” Mun ci amanar Ƴaƴan mu na kin maida hankali wajen basu tarbiyya nagari kamar yadda mu iyayen mu suka yi mana.
” Yara yanzu sun zamo tambaɗaɗɗu, babu tarbiyar arziki tare da su. Dole iyaye su maida hankali wajen kula da tarbiyar ƴaƴan su domin abin yanzu ya tabarbare matuka a kasar nan kuma laifin mu ne iyaye.
Kalaman da Minista Zainab ta rika yi kenan a wajen taron da gwamnatin Kaduna ta shirya inda sarakunan jihar 77 duk suka halarta.
Minista Zainab ta yaba wa gwamnatin Kaduna ƙarƙashin Nasir El-Rufai kan wasu muhimman tsare-tsare da gwamnatin ta kirkiro don taimaka wa matasan jihar.
Ta ce gwamnatin tarayya ta bude gidauniyar naira biliyan 70 domin samar wa matasa ayyukan yi da suka hada da sana’o’in hannu da tallafi don bunkasa sana’o’i ga wadanda suke da abin yi.
Ta yi kira ga matasa da su bibiyi wannan shiri na gwamnati domin cin moriyar sa.
Ana shi jawabin Ministan Embaromen, Muhammad Mahmood, shima kira yayi ga matasa da su rika nesanta kansu daga afkawa cikin munanan dabi’u.
Ita ma mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Hadiza Balarabe, kira tayi ga matasa kada su rika jefa kansu cikin ayyukan ta’addanci, shaye-shaye da shedanci.
Ta yi tsokacin akan kokarin gwamnati ta keyi na cafke wadanda suka fasarfasa rumbunan ajiyan kayan tallafi na Korona a jihar tana mai cewa lallai gwamnati za ta tabbata an taso keyan wadanda suka aikata haka don a hukunta su.
Gwamnonin Sokoto, Aminu Tambuwal, Ekiti Kayode Fayemi da Muhammadu Badaru na Jigawa, duk sun halarci wannan taro.