Ministan Harkokin Cikin Gidan Najeriya, Rauf Aregbesola ya shawarci ‘yan Najeriya da ke kasuwanci a Ghana su ci gaba da zaman su a kasar, kada su dawo Najeriya, kasar yadda su ke niyyar dawowa.
Ministan ya ce su daure su zauna, su bar gwamnatin Najeriya ta ci gaba da tattaunawa da takwarar ta ta Ghana da sauran hukunomin da abin ya shafa, domin a warware matsalar da ta dabaibaye su.
Ranar Laraba Aregbesola ya bada shawarar a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Kungiyar ‘Yan Kasuwa Mazauna Ghana na Najeriya su ka kai masa.
Tawagar na karkashin jagorancin shugabancin Ken Ukaoha, wanda shi ne shugaban kungiyar.
Ministan ya ce gwamnatin Buhari za ta ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Ghana somin a kawo karshen matsalolin da su ke damun su.
Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ta damu kwarai da halin da ‘yan kasuwar na Najeriya ke ciki na rashin jin dadi.
A kan hakan ya jaddada masu cewa gwamnati ba za ta zura ido ta bar su a cikin tasku ba.
“Ba za a ci gaba da zama cikin irin wannan halin kunci da matsin-lamba da ku ke ciki a Ghana ba. Za mu yi duk abin da za mu iya a gwamnatance domin magance maku wadannan matsaloli.” Inji Arwgbesola.
Tun da farko sai da shugaban tawagar, kuma Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwar Najeriya masu harkoki a Ghana su ka zayyana wa ministan irin halin taskun da su ka sha, sanadiyyar kulle masu kantina da aka yi tun cikin 2019, har yau ba a bude masu ba.
Watannin da ya gabata, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labari na musamman kan halin taskun da ‘yan kasuwar Najeriya mazauna Ghana ke ciki, abin da ke da nasara da tsatstsauran biyan haraji da kuma dalilai na cutar korona da su ka ce sun kusa durkusar da ‘yan kasuwar dungurugum, har su ka dauri aniyar dawowa Najeriya.
Discussion about this post