Shugaban Ma’aikata a ofishin Gwamnan Jihar Bauchi, Dakta Ladan Salihu, ya bayyana shirin nan na tallafin matan karkara da kuɗi, wato ‘Rural Women’s Cash Transfer Programme’, da cewar shiri ne na ceton rai a jihar.
Dakta Salihu ya faɗi haka ne cikin wata hira da aka yi da shi, inda ya ce dukkan matan da su ka amfana daga shirin sun samu sana’ar yi ta hanyar tattalin jarin da su ka samu daga shirin.
Ya ce: “Na yi amanna da cewa wannan shiri zai cimma manufofin da aka kafa shi domin su idan aka yi la’akari da irin masu cin moriyar sa a Jihar Bauchi.
“Bari in faɗa maku abin da na fahimta game da wannan shiri. Lokacin da na ke wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan bincike kafin mai girma Minista ta iso, akwai mata sama da 1,200 da su ke jira a waje. Na ga wasu matan kimanin guda 50 waɗanda tun farko ba su yi rajista da shirin ba ko ba a ɗau sunan su ba. Sai na ce kawai a ba su dama su shigo ciki.
“Wasu daga cikin matan guragu ne, da sauran nau’o’i na naƙasa.
“Abin da ya ba ni mamaki da sha’awa shi ne lokacin da na shigo, yawan matan da na gani a ciki su ne a waje. Duk sai aka shigar da su, aka ɗau sunayen su, yanzu sun shiga cikin masu cin moriyar shirin.
“Ina so in taya Mai Girma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari murna kuma in yi jinjina ga mai girma Minista Sadiya Umar Farouq saboda wannan muhimmin shiri na ceton rayuwa wanda ya ke gyara rayuwa tare da inganta ta.”
A kan batun kayan aiki da hanyoyin raba tsabar kuɗin a Jihar Bauchi, Dakta Salihu wanda a da shi ne Darakta-Janar na Hukumar Rediyon Tarayya ta Nijeriya, ya bayyana gamsuwa kan hanyoyin da ake bi ana zaɓar matan da ke amfana da shirin.
Ya ce: “Na gamsu matuƙa da irin shirye-shiryen da aka yi, da kayan aikin da dukkan tsarin da ake bi da yadda aka gudanar da aikin cikin tsanaki ba tare da wani cikas ba.
“Tare da ni aka yi aikin rabon kuma ina tabbatar maku cewa, daga abin da na gani, na gamsu babu wata tantama cewa manufofin wannan shiri ana tsara su ne a tsanake kuma a aiwatar da su ta ingantacciyar hanya.”
Sama da mata 4,000 a ƙananan hukumomi 20 da ke Jihar Bauchi ne kowacce za ta karɓi N20,000 a ƙarƙashin wannan shiri wanda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta shirya domin ceto marasa ƙarfi daga ƙangin talauci.
Zuwa yanzu, sama da mutum 78,000 ne su ka amfana daga tsare-tsaren rage ƙuncin rayuwa a Jihar Bauchi.