Matasan kabilar Ijaw sun ce kada gwamnonin Kudu-maso-kudu su karbi kason kudi gada hannun gwamnatin tarayya

0

Shugaban Majalisar Matasan Ijaw, Peter Igbifa, ya shawarci gwamnonin Kudu kada su karbi kason wata-wata da gwamnatin tarayya ke rabawa a kowane karshen wata.

Ya ce ya kamata gwamnonin su koya wa gwamnatin tarayya darasi, saboda wulakanta yankin da aka yi, inda tawagar Fadar Shugaban Kasa, ta gwasale su, ta ki halartar taron.

Ya ce lokacin da gwamnonin za su koya wa Buhari dasari ya yi, sauka kawai su fara yi masa tilawa.

Domin su nuna wa Buhari fushin su, shugaban na matasa ya ce hatta kashi 13 cikin 100 na rarar ribar man fetur da ake ba su, to kada su karba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda gwamnonin yankin kudu maso kudu su ka nemi fadar shugaban kasa ta ba su hakuri, bisa kin halartar taron da ta shirya da manyan yankin.

Igbifa ya yi fito tsakiyar taro a ranar Talatar da taron bai yiwu ba, ya rika babatu a gaban shugabannin yankin Neja-Delta, inda ya yi kaca-kaca da shugaba Buhari.

An nuno bidiyon, wanda ya rika bambami da hayagaga a gaban Gwamnonin Ribas, Akwa Ibom, Cross River, Edo da kuma Delta.

Sannan kuma ya yi kaca-kaca da ‘yan yankin wadanda su ka karbi mukamai a hannun gwamnatin Buhari. Ya ce duk miyar su ta zaben 2023 su ke gyarawa.

Ya ce lokaci ya yi da za a daina raina masu wayau haka nan.

Ranar Laraba ne dai Shugabannin Kudu-maso-kudu sun nemi Buhari ya ba su hakuri kan “watsa masu kasa” da su ka ce ya yi masu.

Shugabannin Kudu-maso-kudu sun yi kira ga Fadar Shugaban Kasa ta ba su hakuri a rubuce, dangane da taron da ta shirya yi da shugabannin a ranar Talata, amma daga baya ta soke.

Fadar Shugaban Kasa ta soke taron ba tare da bayar wa wani dalili ba, bayan da gwamnonin jihohin da sauran shugabannin yankin sun kammala shirya taron a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Gwamnan Jihar Delta kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu-maso-kudu, wanda ya halarci taron a Fatakwal, shi ne ya shaida wa sauran gwamnoni, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa, matasa da matan yankin cewa Fadar Shugaban Kasa ta aiko cewa ba za ta samu damar halartar taron wanda ita fadar ce ta shirya shi ba.

Okowa ya ce fadar ta ce ta soke taron ne saboda taron gaggawa kan matsalar tsaro da aka yi.

Wannan labarin soke taro ya bakanta wa shugabannin yankin rai matuka, inda su ka fassara abin da muzantawa, cin fuska, cin zarafi, wukakanci da kuma bada wa yankin kura a ido.

A kan haka ne su ka ce daukacin al’ummar yankin Kudu-maso-kudu arankatakaf din su na so Fadar Shugaban Kasa ta nemi afuwa daga yankin.

Sun ce abin da aka yi wa yankin wulakanci ne da kuma nuna gwamnatin tarayya da Fadar Shugaban Kasa ba su dauki yankin Kudu-maso-kusancin kasar nan da muhimmanci ba, duk kuwa da irin muhimmancin da gare shi a kasar nan.

Sai dai kuka Gwamna Okowa ya roki manya da kananan jama’ar yankin su kwantar da hankalin su, su taushi zukatan su daga wannan cin mutunci da aka yi masu.

Ya ce su ma gwamnonin abin ya dugunzuma su, kuma za su isar da sakon bacin ran su da na al’ummar yankin a Fadar Shugaban Kasa.

Idan ba a manta ba, Fadar Shugaban Kasa ta yi makamancin wannan taro a Kaduna da shiyyar Arewa maso Yamma.

Sannan kuma ta yi makamancin sa da shugabanni da gwamnonin yankin Kudu-maso-gabas.

Share.

game da Author