Gwamnan Ebonyi David Umahi ya maida wa gwamnan Wike martanin cewa shi Wken ya maida jam’iyyar PDP kama gidansa, sai yadda yayi da ita.
” Yadda Wike yake yi a PDP ya sa sauran gwamnonin PDP basu kaunar Jam’iyyar da shi kansa.
Sannan Kuma ya gargadi Wike da ya ja bakin sa yayi shiru tsit tunda wuri domin idan ya ce tone-tone za a yi shine zai kwan ciki.
” Ka ja bakin ka kayi shiru tunda wuri, gargadin da nake maka kenan Wike, domin idan ka ce za ka rika wage baki ne kana suka na, toh za a yi tone-tonen da ba zai yi maka dadi ba.
” Wike abokina ne, bana son in yi cacan baki da shi, amma dai ina son ya sani cewa, yana nuna wa duk wani dan jam’iyyar iko ne kamar dakin sa kuma gwamnonin jam’iyyar basu jin dadin sa ko kadan. Sannan ya ce wai na nada kanina shugaban jam’iyyar PDP a jihar, nine nake dawainiya da PDP a yankin Kudu-Maso-Gabas, amma kuma shi ma ya manta cewa shine ya dora shugaban PDP da karfin tsiya, Secondus ko.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin martani da Wike ya maida wa Umahi tun farko ficewarsa daga PDP, inda yace kwadayi ne ya kaishi APC ba wai don ya gaji da PDP ba.
” Mune gwamnan Ebonyi Umahi zai kantara mana karyar wai saboda PDP ta ci amanar Inyamirai ne ya sa ya fice da jam’iyyar ya koma APC. Kada ya kuskura ya fake da haka, shi dai shugabancin Najeriya yake so APC ta bashi takara, akwai wandanda suka kwakwadi lagwadan romon PDP ne irin Inyamirai ne.
Wadannan sune irin kalaman da gwamnan jihar Ribas Nysome Wike ya rika furtawa tun bayan bayyana canja sheka da gwamnan Ebonyi yayi daga PDP zuwa APC.
Gwamnan Ebonyi David Umahi ya sanar da ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC ranar Talata, inda ya ce nuna wariya Kyama da rashin yi wa ƴan kabilar Igbo, wato Nyamirai adalci a jam’iyyar ya sa hakura da ita ya koma APC.
” Tun 1999 ake ta gafara ga shanu nan amma haryan zu ko sawun sa ba mu gani ba. Bayan irin rungumar gani kashe ni da muka yi wa jam’iyyar PDP a kasar nan. Wannan shine babban dalilin da yasa na ga ba zan cigaba da biye wa yaudarar PDP ba da ni da sauran ƴan uwana Inyamirai.
” Bayan haka ina so in fede muku biri saga kai har wutsiya kusani cewa, ban taba neman kujerar shugaban kasa ba ko kuma wai PDP ta tsaida ni dan takara. Musu wannan magana su sani ba a taba haka ba. Idan ma haka ne ai deliget akalla 8000 ne za su yi zabe ba ni zan zabi kai na ba.
” Tsakani da Allah abin kunya ne da cin fuska ace wai tun daga 1999 PDP ba zata iya tsaida dan kabilar Igbo yayi takarar shugaban kasa ba duk da irin goyon bayan da yankin ta rika ba jam’iyyar.
Umahi ya kuma karyata masu cewa wai anyi masa alkawarin wata kujera ce a APC cewa ba bu magana mai kamar haka tsakanin sa da APC, ya ce shi dai yafi gani kila APC ta fi yi wa Inyamirai adalci a nan gaba fiye da PDP da yankin tayi ta bauta mata fiye da shekaru 20.
Sai dai kuma Wike ya tada jijiyoyin wuya kan wadannan kalamai inda ya ce PDP ta rufa wa Inyamirai asiri a tsawon shekarunta na mulki.
Ya ce PDP ta ba Inyamirai damar zama shugaban majalisa har sau uku, sakataren gwamnatin tarayya da manyan mukamai da dama a Jam’iyyar, sannan shi kasa Umahi din a jam’iyyar PDP ya zama gwamna har sau biyu.