Majalisar Kolin Musulunci (NSCIA), wadda a Turance ake kira National Supreme Council for Islamic Affairs, ta sake rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Muhammad Adamu da Babban Daraktan Hukumar Tsaro ta SSS wasika, dangane da zargin kisan-gillar da aka yi zargin an yi wa Musulmai a Kudu maso Gabas da Kudu maso Yammacin Najeriya.
NSCIA, wadda ita majalisa mafi girma da ke wakiltar lamurran da su ka jibinci Musulmai a kasar nan, ta bayyana cewa ya zama tilas ta sake rubuta wa shugabannin tsaron wannan wasika, sakamakon rahotannin da wasu su ka kai cewa an kai masu munanan hare-hare a Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas.
Cikin makonnin nan an samu rahotonnin da ke nuna cewa an kai wa Musulmi hare-hare a Kudancin Najeriya.
An rika watsa wasu hotuna a jaridun online masu nuna an kai wa Musulmai hari tare da hi masu ciwo da kuma banka wa masallacin su wuta a Orlu, cikin Jihar Imo.
Kakakin Yada Labaran ‘Yan Sanda a Jihar Imo, Ikeokwu Orlando, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa rundunar su tsara komai domin tabbatar da cewa duk wani dan kowace kabila ya samu kariya a jihar.
Cikin makon da ya gabata, jaridar The Cable ta buga labarin kona masallatai biyu a garin Nsukka da ke jihar Enugu, biyo bayan wata tankiya da ta faru tsakanin wani dan Keke NAPEP, har dangin wata mata su ka ji masa ciwo saboda rikici ya hada shi da matar, kan rashin cika masa kudin sa ya dauke ta.
Amma kakakin ƴan sandan Enugu, Daniel Ekea, cewa ya yi ba zai yi magana har sai ya tabbatar da afkuwar lamarin tukuna.
Wasikar Nuna Damuwa:
Cikin wasiku daban-daban da NSCIA ta aika wa IGP da SSS, wadanda mataimakin sakataren majalisar, Salisu Shehu ya sa wa hannu, ya nuna cewa irin yadda aka dauko kisan tiryan-tiryan kuma daki-daki, abin damuwa ne.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da su “kare rayuka, dukiyoyi da masallatan Musaulmai a Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma.”
Wasikar ta kuma yi kira da a duba lamarin wadanda aka ragargaza wa dukiyoyi. Ta kuma yi kira shugabannin tsaron su tashi tsaye su dakile barazanar da ake wa Musulmi da dukiyoyin su a yankunan biyu.