Majalisar Dattawa ta nemi a bayar da kashi 1 na harajin-jiki-magayi ga jihohin da tarzomar #EndSARS ta fi yi wa illa

0

Majalisar Dattawa ta nemi Gwamnatin Tarayya ta bayar da kashi 1 bisa 100 na harajin jiki magayi (VAT) ga jihohin da aka fi yin barna lokacin zanga-zangar #EndSARS.

Jihohin da aka fi yi wa barnar dai sun hada Lagos, Ondo, Cross River da Akwa Ibom.

Majalisar ta ce jihohin za su yi amfani da kudaden ne domin gyaran wuraren da aka barnata.

Wannan bayani ya zo ne kwana daya daidai bayan da Majalisar Birtaniya ta nemi gwamnatin Birtaniya ta kakaba takunkumi kan shugabannin Najeriya da aka samu da laifin take hakkin jama’a a lokacin tarzomar #EndSARS.

Rokon a bai wa jihohin kashi 1 bisa 100 na VAT ya taso ne daga rokon da Sanata daga Legas, Olujimi Tunde da kuma Gershorn Bassey na Cross River su ka yi.

Biodun Olujimi ya nemi a bayar da kashi 1 bisa 100 na harajin VAT ga jihar Legas.

Olajimi ya ce Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Lagos ya kiyasta kadarorin da aka lalata wa jihar sun kai na naira tiriliya 1.

PREMIUM TIMES ta buga yadda ‘Yan Majalisar Birtaniya sun nemi a kakaba wa Najeriya takunkumi, saboda “bude wa masu zanga-zanga wuta”.

Majalisar Birtaniya ta nemi kasar ta kakaba wa shugabannin Najeriya da aka samu da laifin bude wa masu zanga-zanga wuta a Lekki, Lagos.

A zaman Majalisar na ranar Litinin, sun yi tattaunawa mai zafi kan Najeriya, inda wadanda su ka yi kakkausan bayanai kan zargin take hakkin jama’a, hana zanga-zanga ta lumana da bude wa masu zanga-zanga wuta, su ka nemi gwamnatin Birtaniya ta haramta wa shugabannin Najeriya shiga kasar, kuma ta kwace dukiyar duk wanda ke da hannu wajen tura sojoji su bude wa masu zanga-zanga ta lumana wuta a Lekki.

Wannan bayani na su ya biyo bayan wata takardar korafi ce ta e-mel da mutum 220,330 su ka sa wa hannu cewa su na goyon bayan Birtaniya ta kakaba wa Najeriya takunkumi.

Cikin wadanda su ka sa wa takardar hannu, sama da mutum 2000 ‘yan Najeriya ne mazauna Birtaniya.

Sun ce dabbanci ne da kuma azabtarwa a iske masu zanga-zanga sun yi dafifi a wuri daya, ba dauke da makamai su ke ba, amma a da sojoji su bude masu wuta.

A zaman Majalisar ta Birtaniya, an zauna a lokacin da mai kula da harkokin Afrika, Theresa Villiers ba ta nan.

Share.

game da Author