Majalisar Dattawa da Ministan Shari’a sun nuna rashin sanin yadda CBN ya kulle asusun wasu masu zanga-zanga

0

Majalisar Dattawa da Ministan Shari’a sun nuna rashin sanin yadda CBN ya kulle asusun wasu masu zanga-zanga.

Kwanaki bayan Babban Bankin Najeriya, CBN ya nemi Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta kulle asusun ajiyar kudaden wasu mutum 20 saboda zargin hannun su wajen zanga-zangar #EndSARS.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda CBN ta nemi iznin kulle asusun wasu da ake zargin su ne su ka shirya zanga-zangar #EndSARS, har su 20.

Bayan kammala taron kwamitin, manema labarai sun tare Minista Malami, inda su ka nemi jin dalilin kulle asusun matasan.

Shi ma Shugaban Kwamitin na Shari’a da Kare Hakkin Jama’a, ya bayyana a zaman kwamitin cewa shi ma bai san da batun za a kulle masu asusun wasu da ake zargin sun shirya zanga-zangar #EndSARS.

Shugaban Kwamiti ya ce ma sai dai a labarai ya ji batun.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da Fadar Shugaban Kasa ta ce wadanda su ka shirya zanga-zangar EndSARS, za su dandana kudar su.

Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa dukkan masu hannu wajen kitsa zanga-zangar #EndSARS, wadda ta rikide ta zama tarzomar da ta haddasa kisa da asarar dukitoyi, za su dandana kudar abin da su ka aikata.

Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, lokacin da ake zantawa da shi a Gidan Talbijin na Channels, da dare a Abuja.

Shehu ya ce tabbas masu zanga-zangar dole su fuskanci shari’a.

“Kasar nan shugaba daya gare ta. Kuma kundin doka daya ta ke da shi. Buhari ne wuka da nama. Kuma komai na kan tebur din sa.

“Dokar kasa ta amince da zanga-zanga, amma idan ta wuce-gona-iri ta zoma tarzoma, to wannan kuma sai doka ta bi wa jama’a da kasa baki daya hakkin su.

” Kowa ya shaida irin mummunar barnar da aka yi aka daka wasoson kayan jama’a da na gwamnati, musamman a Lagos, Calabar, Filato, Taraba da wasu jihohi har da Abuja.

“To yanzu tilas mu kyale doka ta yi aikin ta. Ba ina magana ba ne kan wadanda su ka assasa zanga-zanga. Amma ina magana ne kan mummunar barnar da aka yi a Najeriya. Kuma wadanda su ka haddasa wannan barna sai sun gane kuskuren su.”

Share.

game da Author