Maharan da suka yi garkuwa da matar kwamandan ‘yan bijilante Abdullahi Suleiman su sako ta ranar Litini da dare.
Majiya ta shaida wa PREMIUMTIMES cewa an sako Husna matar Suleiman mai shekaru 50 bayan an biya Kudin diyyan Naira miliyan 2.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Audu Jinjiri, bai tabbatar ko an biya kudin famsar ba sai dai yace maharan sun sako Husna da karfe 10 na daren Litini.
Bayan haka a ranar Talata wani makusancin iyalan Suleiman ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigan sun bukaci a biya su kudin fansa har naira miliyan 50, daga baya dai aka samu suka amince a biya naira miliyan 2.
Ya ce ‘yan bindigan sun tsare Husna da sauran mutanen da suka yi garkuwa da su a dajin Ringim.
Husna na gida tare da iyalinta cikin koshin lafiya.
PREMIUM TIMES ta buga labarin Yadda mahara suka afka har gidan Suleiman suka arce da matarsa a makon jiya.
Discussion about this post