Mahara sun sace Ƴan sanda 12 a Titin Katsina-Zamfara

0

Masu garkuwa da mutane sun sace ƴan sanda 12 a titin Katsina-Zamfara, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Wannan garkuwa da aka yi da ‘Yan Sandan ya faru ne kwanaki 10 da suka wuce.

BBC ta ruwaito cewa, matar daya daga cikin ‘Yan sandan da aka yi garkuwa da su ta kai karar rashin ji daga mijin ta kwana uku da suka yi magana da shi ta waya. A nan ne aka sanar mata cewa anyi garkuwa da mijinta.

Haka kuma daya daga cikin matan wanda aka sace, ta sanar cewa maharan sun tuntube su, sun nemi su aika musu da naira 800,000 kudin fansa kafin su saki mijin ta.

Kakakin rundunar ‘Yan sanda, Frank Mba, bai amsa waya ba a alokacin PREMIUM TIMES ta nemi ji daga bakin rundunar.

Jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara sun yi kaurin suna wajen hare-haren ‘yan bindiga da kuma garkuwa da mutane.

Haka Kuma titin Abuja zuwa Kaduna shima ya zama abin tashin hankali. Kusan Kullum sai an yi garkuwa da mutane.

Share.

game da Author