Mahara sun kashe ƴan ƙungiyar bijilante uku, sun ji wa biyu rauni a Kaduna

0

Mahara a kauyen Dande dake karamar hukumar Chikun sun kashe wasu ƴan banga har su uku sannan sun ji wa wasu biyu raunu a harin kwantar bauna da suka kai wa ƴan bangan a yankin Bukuru dake jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya sanar da haka a wata takarda da fitar ranar Laraba da yamma.

Aruwan ya ce maharan sun bude wa wasu ƴan banga wuta ne a harin kwantar bauna da suka kai musu a hanyar Dande dake yankin Buruku.

Mutum uku sun rasu sannan wasu mutum biyu cikun ƴan bangan sun samu rauni.

Sai dai kuma sanarwar ta cigaba da cewa jim kadan bayan afka wa ƴan bangan da maharan suka yi, sojojin saman Najeriya da ke aiki a yankin suka diran musu ta hanyar yi musu luguden wuta daga sama suka yi fatafata da su sannan suka ragargaza sansanonin su a yankin.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya aika da sakon jaje ga iyalai da ƴan uwan wadanda suka rasu da wadanda suka ji ciwo a arangamar.

Sannan kuma ya jinjina wa sojojin da suka kai wa ƴan bangan dauki cikin gaggawa da kuma ya a musa kan ayyukan da suke yi na kawo zaman lafiya a jihar.

Share.

game da Author