Magu ya koka kan yadda kwamitin bincike ke kiran shaidu ta bayan-fage

0

Lauyan tsohon shugaban EFCC Ibrahim Magu ya bayyana koken sa dangane da yadda Kwamitin Bincike karkashin shugabancin Tsohon Mai Shari’a Ayo Salami ke ci gaba da gabatar da shaidu, duk kuwa da cewa shi Magu ya kammala kare kan sa a gaban kwamitin.

Premium Times ta sha buga labaran yadda a baya Magu ya sha zargin kwamitin Salami da kin amincewa ya gabatar da na sa shaidun a gaban kwamiti, kuma Salami ya ki amincewa ko wasikar gayyata a aika wa shaidun da shi Magu din ke nema ya gabatar.

Lauya Shittu ya aiko wa PREMIUM TIMES takardar da ya fitar a ranar Laraba cewa, duk da Magu ya kammala gabatar da bayanai da kare kan sa a bayan fage, makonni shida da su ka gabata, har yanzu su Salami na kiran na su shaidu ta bayan-fage, ba tare da sanin Magu ba.

“Irin yadda kwamitin Salami ke karakainar gayyatar wadanda ake tuhuma da laifi, wadanda EFCC ta gurfanar domin su bayar da shaida kan Magu a bayan idon sa, haramtacciyar hanya ce da ta saba wa dokar Najeriya. Kuma ta nuna rashin adalci kuru-kuru ga tsarin sauraren bangarori biyu, musamman na wanda ake kara.”

“Idan za a gabatar da shaida kan wanda ake zargi, to tilas zai kasance ya na wurin. Idan kuwa aka dauki bayanan mai gabatar da shaidar da ke kokarin dora laifi kan wanda ake zargi, ba tare da wanda ake zargin ya na wurin ba, to wannan karan-tsaye ne aka keta rigar mutuncin shari’a.

“Don haka matsawar aka yanke hukunci a bisa karbar bayanan irin wadannan makafin shaidu, to tilas Kotun Daukaka Kara ta jingine wannan shari’a, domin makauniya ce.

“Haka dai Sashe na 76 na Dokar Gabatar da Shaida ta 243 ta gindaya.”

Shittu ya ci gaba da rattaba zarge-zarge masu yawa kan Ayo Salami, wanda ya nuna cewa kwamitin ya zama shirme kenan, domin ko ya yanke wa Magu hukunci, to Kotun Daukaka Kara jingine hukuncin za ta yi.

Matsalar kwamitin Salami ba shi da kakakin yada labarai ballantana a ji ta bakin sa.

Sannan kuma tun da aka kafa kwamitin an hana ‘yan jarida shiga, balle a san wainar da ake toyawa a wannan zaure.

Share.

game da Author