MAFITAR KARAYAR TATTALIN ARZIKI: Atiku ya nemi a tsawwala wa gaggan attajirai haraji

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya shawarci gwamnatin Najeriya ta kara wa attajiran kasar nan haraji mai kauri, yadda za a samu kudaden shigar da za su ceto kasar nan daga karayar tattalin arzikin da ta afka.

Bayan buga labarin karayar tattalin arzikin, PREMIUM TIMES ta kuma buga sharhin yadda za ka iya gane ko karayar tattalin arzikin Najeirya ya shafe ka kai-tsaye.

Najeriya ta sake ruftawa cikin kunci da matsin tattalin arzikin da shekaru 40 ba ta shiga ba.

A karo na biyu tun bayan 2016, Najeriya ta sake afkawa cikin tabarbarewar tattalin arziki, yayin da ake shirin afkawa ramin da shekaru arba’in ba a shiga kunci irin sa ba.

A karo na biyu kenan, tattalin arzikin na Najeriya ya sake tabarbarewa, bayan ya tabarbare shekaru biyar da su ka gabata. Watanni shida kenan Malejin Bunkasar Tattalin Arzikin Cikin Kasa (GDP) ya yi tsaye cancak, ya kasa gaba. A gefe daya kuma sai tiriliyoyin bashi gwamnatin Buhari ke ta kara labtawa kan gadon bayan tabarbararren tattalin arzikin.

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), wadda hukuma ce ta gwamnatin tarayya, ta bayyana wannan labari maras dadin ji.

NBS ta ce tsawon watanni shida kenan tattalin arzikin Najeriya ya kasa motsawa gaba. Har yau a kashi 3.62 ya ke, ga shi an shiga wasu wasu watanni uku masu hatsari, ga shi kuma 2020 ta na gab da karewa, sannan kuma za a shiga shekarar 2021 za a shiga, shekarar likimon bashi a wuyan Najeriya.

Baya ga bashin sa Najeriya ke kara labtawa kan ta, kusan rabin kudin da Najeriya ke samu a duk wata, ya na tafiya ne wajen biyan basussuka da kuma biyan kudin ruwan basussukan da ba kai ga fara biya ba.

Yadda Mai Karatu Zai Iya Gane Ko Karayar Arzikin Najeriya Ya Shafe Shi:

Karayar tattalin arziki na afkawa kan kasa idan tattalin arzikin ta ya ci gaba da dulmiyawa kasa maimakon ya yi sama, har tsawon watanni shida a jere.

To idan aka kai ga wannan mataki, ko kuma aka zarce a haka tattalin arziki ya tashi daga karyewa, ya kai ga tabarbarewa.

Ana auna karfin tattalin arzikin kasa da karfin nauyin awon sikelin GDP na kasar. Shi kuwa GDP, shi ne karfin darajar abin da kasa ke samarwa ko ta ke kerawa ko kirkira a cikin kasar, ba tare da ta dogara da na kasar waje ba, har tsawon shekara guda.

Zuwa karshen Satumba sai karfin tattalin arzikin cikin gida na Najeriya (GDP), ya kai darajar naira tiriliyan 39, kuma shi ne mafi karfi a dukkan kasashen Afrika.

Idan tattalin arziki ya bunkasa, to al’ummar kasa kan kara samun karuwar arziki, a samu karin arrajirai, a samu aikin yi, albashin ma’aikata ya karu, rayuwa ta inganta, kuma a samu yalwar arziki.

Sannan kuma masu zuba jari a masana’antu, cibiyoyin hada-hada da harkokin kasuwanci su kara samun riba.

Gwamnati na karuwa idan tattalin arziki ya bunkasa, ta hanyar karin samun kudin shiga na haraji daban-daban. A gefe daya kuma zai kasance gwamnati na da tulin kudi ajiye dankam, wadanda za ta rika kaahewa wajen gudanar da ayyukan inganta al’umma da raya kasa, ba tare da wata jikarar sai ta jira ta ciwo bashi ba.

Yadda Kasa Ke Ruftawa Kogon Ramin Karayar Tattalin Arziki:

Idan aka samu kasa na ci baya har tsawon watanni uku sau biyu kuwa, wato watanni shida a jere, to kafafun sa biyun da ya ke tsaye da su sun yi sanyi kenan. Ba su da nauyin daukar lodin matsalolin da su ka dabaibaye tattalin arzikin kasar.

Wannan kuwa gagarimar matsala ce ga kowace kasa duk karfin ta a duniya.

Rabon da Najeriya ta samu kan ta a wannan yanayi tun cikin 2015/2016.

Manyan Dalilai:

Manyan dalilai dai ba su wuce yawan bashin da ya kumbura wa Najeriya ciki, har numfashi mai karfi ke neman gagarar tattalin arzikin kasar. Akwai kuma karancin kudi a aljihun gwamnatin tarayya.

Shawarar Atiku Abubakar:

Da ya ke bayani kan karayar tattalin arzikin, Atiku ya ce bai yi mamaki ba, amma fa abin ya dame shi sosai.

Sai ya ce laifin Buhari ne da tun farko ba ya jin shawara, tunda an shemawarce shi a rage yawan kudin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.

Ya ce an kuma shawarci Buhari ya rage yawan ciwo bashin da ya ke yi a kasashen waje, amma kamar kara ingiza shi ciwo bashin ake yi.

“Tabbas barkewar korona ya kara barke aljihun Najeriya. Amma da an rage kashe kudade da facaka wajen tafiyar da gwamnati da kuma taka wa ciwo bashi burki, to da an samu saukin abin sosai.”

Da ya ke magana kan mafita, baya ga karin haraji kan masu karfi, Atiku ya ce kasafin naira tiriliyan 13 da gwamnatin Buhari ta yi na 2021, holoko kawai, domin babu kudin. Haraji ne na kawai “na kayan alatu.” Don haka ya ce da kamata ya yi a diba daidai yadda baki zai iya dauka kawai.

Ya kara kawo shawarar tallafa wa talakawa ta hanyar rika tura N5,000 a asusun bankin kowane talakan da a shekara abin da ke cikin asusun bai wuce adadin mafi kankantar albashi ba.

Ya kuma bada shawarar a dora haraji a kan kayan alatu wadanda sai tajirai ne kadai ke iya sayen su.

Share.

game da Author