Ma’aikatar Jinkai da Inganta Rayuwa ta bayyana cewa ma’aikatar ta ta ciyar da gidaje 127,588, a lokacin Kullen Korona a kasar nan.
Ma’aikatar ta ce wannan kason yaran makaranta ne da ake ciyarwa aka bi su har gida aka baiwa iyayen su a lokacin Kullen korona.
A cikin kowane buhu da aka raba wa iyayen yara, akwai shinkafa, mangyada, Manja, Gishiri, Tomatir da Wake.
” Gwamnatocin Jihohi ne suka raba abincin a jihohin su harda babban birnin Tarayya, Abuja.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ma’aikatar ta musanta cewa ba ta amshi gudummawa ko ta sisi ba a nan cikin gida da kuma kasashen waje da suna tallafin korona.
Sadiya ta bayyana baka a lokacin da ta ke kare kasafin ma’aikatar ta na 2021, a gaban kwamitin Majalisar Tarayya.
Ministar ta yi wannan ikirari bayan Najeriya ta karbi bilyoyin kudade a matsayin kudaden gudummawar tallafi da yaki da cutar korona.
Sadiya ta ce ko sisi ba a bai wa ma’aikatar ta ba a cikin kudaden wadanda wasu daidaikun jama’a da kamfanoni su ka bayar gudummawa.
Ya zuwa karshen watan Afrilu, kudaden da Najeriya ta tara daga gudummawa, sun kai naira bilyan 27.160.
Ta ce amma ba a bai wa ma’aikatar ta ko sisi ba.