Kwamitin Majalisa ya ce kasafin rundunar ƴan sanda na naira bilyan 449 ya yi kadan

0

Kwamitin Majalisar Tarayya mai lura da Harkokin ‘Yan Sanda, ya ce kasafin 2021 da aka ware wa hukumar ‘yan sanda naira bilyan 449, ya yi kadan matuka.

Shugaban Kwamitin, Mohammed Kumo ne ya bayyana haka a lokacin da Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ke kare kasafin a gaban kwamitin.

Ya ce a bayyane ya ke cewa ana yi wa ‘yan sanda kwangen kudade, maimakon a rika wadata su da kudaden.

Kan haka ne ya ce kasafin naira bilyan 449 kacal ya yi wa ‘yan sandan Najeriya kadan a shekarar 2021.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya a gaggauta kara wa ‘yan sanda kudi a kasafin 2021. Sannan ya sha wa Sufeto Janar Adamu alwashin cewa a karshen kammala kare kasafin kudi, zai tabbatar an kara wa ‘yan sanda wani kaso mai kauri.

“Kakakin Majalisar Tarayya da Mataimakin sa sun umarce ni da na shaida maka cewa ka kawo sunayen ‘yan sandan da su ka rayukan su sanadiyyar tarzomar #EndSARS.” Inji Kumo.

Ya ce akwai dokokin da su ka dabaibaye aikin ‘yan sanda, wadanda tilas sai an yi watsi da su, domin a yi wa dokoki kwaskwarima a samu a kara inganta aikin dan sanda.

Ya ce kada kuma a manta da umarnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar na a yi wa ‘yan sanda karin albashi. Ya ce shi ma wannan abin jinjina ne.

Sufeto Janar Adamu ya lissafa abin da ya kira “wasu matsalolin da su ka addabi aikin dan sanda da su ka hada karancin kudade, rikice-rikicen da ka taso ba a san da zuwan su na, tarzomar #EndSARS da sauran su.

Ya ce tun da farko naira bilyan 469 aka rubuta a kasafin ‘yan sanda na 2021. Amma sai aka zabtare shi ya koma naira bilyan 449.

Share.

game da Author