Wata cuta da ake zaton cutar kwalara ce ta yi ajalin mutum 8 sannan wasu 10 na kwance a asibiti a jihar Oyo.
Cutar ta bullo a wasu kauyuka dake karamar hukumar Lagelu ta Arewa, dake jihar.
Sakataren karamar hukumar Mudashiru Quamardeen ya tabbatar da haka yana mai cewa da wuya cutar da ta bullo ba cutar kwalara bane.
“Mutum 8 sun mutu sannan 10 na asibiti.
Ya ce alamun da masu fama da cutar suka nuna sun hada da amai da gudawa.
An Kuma wadatar da magungunan kawar da cutar a asibitocin jihar domin a dakile yaduwar ta a fadin jihar.
Quamardeen ya ce an sallami mutum 2 daga cikin mutum 10 din dake kwance a asibiti.
Har yanzu kwamishinan kiwon lafiya na jihar Bashir Bello bai ce komai ba.
Cutar kwalara ko kuma cutar amai da zawo cuta ce dake yawan sa mutum yin bahaya da amai sannan rashin gaggauta daukan mataki kan iya yin ajalin mutum a cikin lokaci kalilan.
Sakamakon binciken kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ya nuna cewa mutane miliyan 2.9 sun kamu da cutar sannan mutane 95,000 sun mutu a kasashen masu tasowa a dalilin wannan cuta.
Alamun kamuwa da cutar kwalara.
1. Zazzabi.
2. Amai da gudawa.
3. Rashin jin karfi a jiki.
4. Rashin iya cin abinci
5. Suma.
Hanyoyin gujewa kamuwa da cutar.
1. Tsaftace muhalli.
2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.
3. A guji yin bahaya a waje.
4. Amfani da tsaftattacen ruwa.
5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.
6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.
7. Yin allurar rigakafi
8. Zuwa asibiti da zaran an kamu da cutar.
likitoci sun yi kira da arika gaggauta garzaya asibiti domin warkar da cutar.
Discussion about this post