Kotun Abuja ta ce Gwamnatin Kogi ta biya tsohon mataimakin gwamnan jihar diyyar naira milyan 180

0

Kotun Abuja ta zartas da hukuncin cewa Gwamnatin Jihar Kogi ta biya tsohon Mataimakin Gwamna Simon Achuba naira milyan 180 wadanda hakkin sa ne da aka hana shi.

Mai Shari’a Oyebiola Oyewunmi ya ce gwamnatin Kogi ta biya shi kudin cikin kwanaki 30. Ya ce idan ba a gaggauta biyan sa kudaden cikin kwanaki 30 ba, to duk wata za a rika dora wa Kogi biyan karin kashi 30 bisa 100 na kudaden, saboda bata masa lokaci.

Achuba ya samu matsala da Gamma Yayaha Bello, inda a karshe Kwamishinan Shari’a na Kogi, Nasir Ajana ya nada kkwamitin binciken sa, aka ce an same da aikata ba daidai ba. Wannan ta sa majalisar Kogi ta tsige shi.

Achuba ya kai kara kotu, inda ya nemi a biya shi hakkokjn sa da Gwamnatin Kogi ta danne masa.

Ya nemi a biya shi naira milyan 921,572,758 matsayin hakkokin sa da Kogi ta danne masa.

Mai Shari’a Oyewunmi ta ce a gaggauta biyan sa naira milyan 180, ko kuma duk wata kudin su rika haihuwar kashi 30% a duk watan da ya kare ba a biya shi ba.

Share.

game da Author