Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa dalibai masu bautan ƙasa, NYSC, 138 sun Kamu cutar Korona.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya Sanar da haka ranar Litini a taron manema labarai da kwamitin shugaban kasa kan Korona, PTF ke yi a Abuja.
Ya ce mutum 138 din da Suka kamu da cutar ba a barsu sun shiga cikin sansanin horas da dalibai ƴan bautan kasa ba.
” Gwajin da akayi wa dalibai da ma’aikata 34,785 ya tsamo ɗalibai 138 da ke dauke da cutar.
Ihekweazu ya ce tuni an garzaya da wadanda suka kamu da cutar kuma ana kula da su a gida bisa ga yanayin tsananin cutar a jikinsu.
Bayan haka Ihekweazu ya ce yayin da gwamnati ke tattaunawa da kungiyar jami’o’in kasar nan hukumar za ta tattauna da malamai domin tsara hanyoyin da za abi don kare dalibai daga kamuwa da cutar a jami’o’in kasar nan.