KORONA: WHO ta yi kira da a tsananta yin gwaji domin dakile yaduwar cutar

0

Shugaban kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO Tedros Gheybreyesus ya yi kira ga gwamnatoci da mahukunta da su tsananta yi wa mutane gwajin cutar Korona, cewa yin haka shine hanyar dakile yaduwar cutar mafi a’ala.

Gheybreyesus ya ce yin haka zai sa a samu nasaran dakile yaduwar korona fiye da yi wa mutane allurar rigakafin cutar.

Ya yi kira ga kasashen duniya da su zage damtse wajen yi wa mutane gwajin cutar koda bayan an fidda maganin rigakafin cutar domin amfanin mutane.

Idan ba a manta ba Shugaban fannin gaggauta dakile yaduwar cututtuka na hukumar WHO Mike Ryan ya gargadin cewa maganin rigakafin cutar korona ba shine kadai zai dakile yaduwar cutar Korona ba.

Ryan ya ce samun maganin rigakafin cutar zai taimaka wajen dakile yaduwar Korona amma idan ba a hada shi da kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar ba za ta ci gaba da yaduwa.

Hanyoyi 10 don gujewa kamuwa da cutar

1. Yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu.
2. Rufe hanci da baki idan za ayi atishawa.
3. A wanke kuma a dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
4. Rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya.
5. A saka takunkumin fuska musamman idan za a fita ko Kuma Ana cikin mutane.
6. Za a iya amfani da man tsaftace hannu Idan Babu wura da sabulu domin wanke hannu.
7. A rika zama a dakin dake da iska ko Kuma fanka.
8. A rika tsaftace muhalli akai akai.
9. A rage yawan fita Idan ba ya saka dole ba.
10. A rage yawan Zama wurin da akwai chinkoson mutane.

Share.

game da Author