Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 157 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum – 97, Oyo-37, Kaduna -9, Bayelsa-3, Edo-3, Ekiti-3, Ondo-2, Osun-2 da Filato -1.
Yanzu mutum 65,305 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 61,162 sun warke, 1,163 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 2,980 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 22,501, FCT –6,371, Oyo – 3,654, Edo –2,688, Delta –1,823, Rivers 2,914, Kano –1,760, Ogun –2,099, Kaduna –2,773, Katsina -965, Ondo –1,722, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 744, Ebonyi –1,055, Filato -3,720, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –648, Jigawa – 325, Kwara –1,084, Bayelsa – 426, Nasarawa – 485, Osun –942, Sokoto – 165, Niger – 283, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 346.
Taraba- 153, Kogi – 5, da Cross Rivers – 89.
Idan kuma ba a manta ba domin a rika samun bayanan gaskiya game da annobar Korona, gwamnati ta samar da lambar waya da za rika tuntuba domin samun bayanan Korona kaitsaye daga hukumar NCDC.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya ce gwamnati da hadin guiwar UNICEF ne suka kirkiro wannan dabara.
Babban makasudin samar da wannan layi shine don mutane su rika samun labaran gaskiya wato sahihan labarai game da Korona.
Mutum zai aika da sakon ‘Coronavirus’ zuwa lambar 24453, daga nan za a aiko masa da sakonni game da cutar da matsayin da duniya ke ciki da kasa Najeriya.
Ihekweazu ya ce gwamnati ta fadada abin zuwa kafafen sada zumuta na Facebook da WhatsApp domin samar wa mutane bayanan cutar.
Domin shiga wannan dandali a facebook ko Kuma WhatsApp za a iya aikawa da sakon ‘Coronavirus’ zuwa ga +234 908 740 1607. Ko Kuma ta adireshin U-Report kamar haka @ureportnigeria Wakilin asusun UNICEF a Najeriya Peter Hawkins ya gargadi mutane da su cigaba da kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar korona cewa yin haka ne kadai mutum zai iya samun kariya daga cutar.
Discussion about this post