Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 59 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa jihar Kaduna ta samu karin mutum –28, Rivers-9, Ogun-8, Ondo-8, Kano-2, Niger-2, Kwara-1 da Filato-1.
Yanzu mutum 63,790 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 59,884 sun warke, 1,154 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 2,752 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 21,655, FCT –6,212, Oyo – 3,515, Edo –2,673, Delta –1,816, Rivers 2,866, Kano –1,755, Ogun –2,075, Kaduna –2,698, Katsina -953, Ondo –1,696, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 717, Ebonyi –1,055, Filato -3,676, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –622, Jigawa – 325, Kwara – 1,072, Bayelsa – 413, Nasarawa – 483, Osun –931, Sokoto – 165, Niger – 281, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 338.
Taraba- 152, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Akwai yiwuwar mai dauke da cutar Korona zai iya afkawa cikin matsalar tabuwar hankali
Likitocin jami’ar ‘University Collage UCL’ dake kasar Birtaniya sun bayyana cewa akwai yiwuwar wanda ya kamu da Korona ya afka cikin hali na jirkitar kwakwalwa.
Jagoran wannan bincike Kuma jami’in UCL Ross Paterson ya sanar da haka yana mai cewa dole a ci gaba da gudanar da bincike domin gano adadin illar da cutar zai iya yi wa mutum.
Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Amma ita cutar Corona Virus sabuwar cuta ce da ba a taba samun ta a jikin mutum ba.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Haka kuma idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
An samar da wasu hanyoyi na gaggawa domin kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
WHO ta yi kira da a rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.