KORONA: Mutum 56 Kacal suka kamu a Najeriya ranar Litinin

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 56 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litinin

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –6, FCT 17, Kaduna-18, Filato-5
Kano-3, Kwara-2, Yobe-2, Ekiti-1, Niger-1
da Rivers-1.

Yanzu mutum 66,439 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 62,241 sun warke, 1,168 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,030 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 22,968, FCT –6,515, Oyo – 3,703, Edo –2,694, Delta –1,823, Rivers 2,957, Kano –1,776, Ogun –2,153, Kaduna –2,913, Katsina -1,007, Ondo –1,727, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 753, Ebonyi –1,055, Filato -3,805, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –662, Jigawa – 328, Kwara –1,093, Bayelsa – 445, Nasarawa – 485, Osun –945, Sokoto – 165, Niger – 296, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 94, Ekiti – 354, Taraba- 157, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.

Bayan haka rahoton bincike da ka yi ya nuna cewa akalla 18.3% na mutanen da cutar korona ta kashe a Afrika cewa na fama da cutar siga wato ‘Dibeties’ a daidai lokacin da suka kamu da cutar.

Kungiyar kiwon lafiya ce ta gudanar da wannan bincike a kasashen Afrika 14.

Sakamakon wannan bincike ya nuna hadarin da masu dauke da ciwon siga ke ciki a wannan lokaci da annobar korona ta dabaibaye duniya musamman ga wadanda ke da shekaru 60 zuwa sama.

An gano cewa mutane da dama da ke dauke da wasu cututtukan sukan fada cikin yanayi na damuwa saboda maida hankali da aka yi kan kauda korona. Wasu cututtukan kuma suna ta cigaba da yaduwa

Share.

game da Author