KORONA: Mutum 236 suka kamu a Najeriya ranar Laraba

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 236 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –142, Ogun-19, Kaduna-15, FCT-14, Imo-14, Rivers-14, Filato-6, Katsina-3, Ekiti-2, Jigawa-2, Oyo-2, Cross River-1, Kano-1 da Taraba-1

Yanzu mutum 65,693 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 61,457 sun warke, 1,163 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,072 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 22,704, FCT –6,399, Oyo – 3,695, Edo –2,690, Delta –1,823, Rivers 2,930, Kano –1,769, Ogun –2,122, Kaduna –2,793, Katsina -968, Ondo –1,722, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 750, Ebonyi –1,055, Filato -3,730, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –662, Jigawa – 327, Kwara –1,088, Bayelsa – 426, Nasarawa – 485, Osun –942, Sokoto – 165, Niger – 283, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 92, Ekiti – 348, Taraba- 156, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.

A ranar 13 ga Nuwanba ne PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda 18.3% na mutanen da cutar korona ta kashe a Afrika na fama da cutar siga wato ‘Dibeties’ a daidai lokacin da suka kamu da cutar.

Kungiyar kiwon lafiya ce ta gudanar da wannan bincike a kasashen Afrika 14.

Sakamakon wannan bincike ya nuna hadarin da masu dauke da ciwon siga ke ciki a wannan lokaci da annobar korona ta dabaibaye duniya musamman ga wadanda ke da shekaru 60 zuwa sama.

An gano cewa mutane da dama da ke dauke da wasu cututtukan sukan fada cikin yanayi na damuwa saboda maida hankali da aka yi kan kauda korona. Wasu cututtukan kuma suna ta cigaba da yaduwa.

Share.

game da Author