Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 110 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –26, FCT-23, Kaduna-20, Katsina-11, Ogun-7, Ekiti-6, Filato-5, Rivers-4, Kano-3, Nasarawa-3 da Niger-2
Yanzu mutum 67,330 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 62,819 sun warke, 1,171 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,340 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 23,190, FCT –6,767, Oyo – 3,721, Edo –2,696, Delta –1,824, Rivers 2,977, Kano –1,794, Ogun –2,222, Kaduna –3,064, Katsina -1,025, Ondo –1,728, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi –770, Ebonyi –1,055, Filato -3,857, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –662, Jigawa – 331, Kwara –1,096, Bayelsa – 445, Nasarawa – 491, Osun –945, Sokoto – 165, Niger – 298, Akwa Ibom – 339, Benue – 496, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 94, Ekiti – 365, Taraba- 159, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
Kasar Birtaniya ta yardan wa kamfanin Pfizer na kasar Amurka da Kamfanin BioNTech na kasar Jamus su fara yi wa mutane rigakafin cutar korona da kamfanonin biyu suka hadauka hada.
Gwamnatin ta bada wannan izini ne bayan sakamakon gwajin sahihanci da ingancin maganin karo na uku ya fito.
Bisa ga sakamakon maganin rigakafin da wadannan kamfanonin suka hada ingancin sa ya kai kashi 95.
Pfizer da BioNTech za su fara yi wa mutane rigakafin cutar ne ranar 1 ga watan Disemba.
Discussion about this post