KORONA: An samu karin mutum 223 da suka kamu a Najeriya ranar Juma’a

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 223 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –85, FCT-35, Akwa Ibom-24, Enugu-18, Filato-13, Rivers-10, Abia-7, Ebonyi-6, Anambra-5, Adamawa-4, Bauchi-3, Imo-3, Ogun-3, Oyo-3, Kwara-2, Osun-1 da Taraba-1

Yanzu mutum 63,731 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 59,844 sun warke, 1,154 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 2,730 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 21,655, FCT –6,212, Oyo – 3,515, Edo –2,673, Delta –1,816, Rivers 2,857, Kano –1,753, Ogun –2,067, Kaduna –2,670, Katsina -953, Ondo –1,687, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 717, Ebonyi –1,055, Filato -3,675, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –622, Jigawa – 325, Kwara – 1,071, Bayelsa – 413, Nasarawa – 483, Osun –931, Sokoto – 165, Niger – 279, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 338.
Taraba- 152, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.

PREMIUMTIMES ta buga labarin yadda gwamnati jihar Neja ta musanta labarin cewa wai wasu kwamishinonin jihar uku sun kamu cutar korona a jihar.

Sakataren gwamnati kuma shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar korona na jihar Ahmed Matane ya karyata haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai ranar 5 ga Nuwanba.

Matane ya ce labaran da ake ta yadawa wai wasu kwamishinoni uku sun kamu da cutar korona a jihar, shirgegen karya ne, kuma ya yi kira ga mutane da su daina yada ire-iren wadannan labarai na karya domin gujewa tada hankalin mutane.

Ya tabbatar cewa gwamnati na iya kokarinta wajen ganin ta ta dakile yaduwar cutar a jihar.

Matane ya yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar a jihar domin Kare kansu.

Share.

game da Author