KORONA: An samu karin mutum 212 da suka kamu a Najeriya ranar Alhamis

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 212 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa jihar Kaduna ta samu karin mutum –71, Imo-26, Filato-26, FCT-19, Ondo-17, Kaduna-14, Rivers-9, Oyo-9, Katsina-6, Osun-4, Bauchi-2, Ekiti-2, Nasarawa-2, Ogun-2, Kano-1, Kwara-1 da Taraba-1.

Yanzu mutum 64,728 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 60,790 sun warke, 1,162 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 2,776 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 22,198, FCT –6,322, Oyo – 3,590, Edo –2,680, Delta –1,816, Rivers 2,890, Kano –1,756, Ogun –2,084, Kaduna –2,739, Katsina -959, Ondo –1,717, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 741, Ebonyi –1,055, Filato -3,705, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –648, Jigawa – 325, Kwara –1,084, Bayelsa – 414, Nasarawa – 485, Osun –936, Sokoto – 165, Niger – 281, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 340.
Taraba- 153, Kogi – 5, da Cross Rivers – 89.

Pfizer ya kammala hada maganin rigakafin Korona, abin da ya rage bai wuce kashi 10% ba

Kamfanin Pfizer dake kasar Amurka da Kamfanin BioNTech dake kasar Jamus sun hada maganin rigakafin kamuwa da kwayoyin cutar korona dake da aka tabbatar da ingancin sa da akalla kashi 90 bisa 100.

Wadannan Kamfanonin sun hada wannan magani ƙasa da lokacin da ake zaton za a kammala hada shi kuma har sun yi gwajin ingancin sa a jikin mutane sama da 44,000.

Kamfanonin na sa ran cewa gwajin ingancin maganin da ake yi ba zai dauki tsawon lokaci ba domin samun izinin fara amfani da maganin.

Share.

game da Author