Korona na cigaba da wawushe mutanen kasar Amurka, wanda zuwa yanzu alkaluma suka nuna cewa sama da mutun 250,000 sun rasu a dalilin kamuwa da cutar.
‘Wordometer’ da ke fidda alkaluman bayanan halin da kasashen duniya ke ciki game da annobar ya fitar cewa ana cigaba da samun hau-hawan yawan mutanen dake kamuwa da cutar a kasar Amurka da kuma wadanda ke rasuwa a kullum.
A makon da ya gabata akalla mutum 1,167 suka mutu a cikin uni daya.
A yanzu dai Amurka ita ce kan gaba wajen samun yawan mutanen da korona ta kashe a duniya.
Mutum miliyan 11.8 me suka mutu a Amurka a yanzu haka.
A yanzu mutum miliyan 56 ne suka kamu da cutar sannan miliyan 1.3 sun mutu a duniya.
Yaduwar cutar a Najeriya
A ranar 17 ga Nuwamba mutum 236 ne suka kamu da cutar a Najeriya.
An yi wa mutu 721,516 gwajin cutar inda daga ciki mutum 65,693 Sika kami da cutar.
An sallami mutum 61,457 sannan mutum 3,072 na asibiti.
Mutum 1,164 sun mutu a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 22,704, FCT –6,399, Oyo – 3,695, Edo –2,690, Delta –1,823, Rivers 2,930, Kano –1,769, Ogun –2,122, Kaduna –2,793, Katsina -968, Ondo –1,722, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 750, Ebonyi –1,055, Filato -3,730, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –662, Jigawa – 327, Kwara –1,088, Bayelsa – 426, Nasarawa – 485, Osun –942, Sokoto – 165, Niger – 283, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 92, Ekiti – 348.
Discussion about this post