KORONA: Adadin yawan mutanen da suka kamu a Afrika ya zarce mutum miliyan biyu

0

Korona na cigaba da yaduwa a Nahiyar Afrika wanda zuwa yanzu alkaluma sun nuna cewa sama da mutum miliyan biyu sun kamu da cutar.

Mutum sama da miliyan 1.7 sun warke sannan mutum 48,000 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.

Ofishin WHO dake Brazzaville kasar Kongo ya sanar da haka.

Zuwa yanzu kasashen Afirka ta Kudu, Algeria da Kenya ne kasashe a nahiyar da suka fi kamuwa da cutar.

Kasar Afrika ta Kudu mutum 757,144 sun kamu, 20,556 sun mutu.

A Algeria mutum 70,629 sun kamu, 2,206 sun mutu.

Kasar Kenya ta samu mutum 72,686 da suka kamu da mutum 1,313 da Suka mutu

Yaduwar cutar a Najeriya

A ranar 19 ga Nuwamba mutum 146 ne suka kamu da cutar a Najeriya.

An yi wa mutu 728,128 gwajin cutar inda daga ciki mutum 65,839 suka kamu da cutar.

An sallami mutum 61,573, mutum 1,165 sun mutu sannan mutum 3,101 na asibiti.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 22,766, FCT –6,422, Oyo – 3,698, Edo –2,690, Delta –1,823, Rivers 2,942, Kano –1,770, Ogun –2,134, Kaduna –2,814, Katsina -970, Ondo –1,727, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 752, Ebonyi –1,055, Filato -3,733, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –662, Jigawa – 327, Kwara –1,088, Bayelsa – 426, Nasarawa – 485, Osun –942, Sokoto – 165, Niger – 283, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 92, Ekiti – 348, Taraba- 156, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.

Kasar Amurka

Labaran da PREMIUMTIMES ta buga ranar 19 ga Nuwanba ya nuna cewa Korona na cigaba da wawushe mutanen kasar Amurka, wanda zuwa yanzu alkaluma suka nuna cewa sama da mutun 250,000 sun rasu a dalilin kamuwa da cutar.

‘Wordometer’ da ke fidda alkaluman bayanan halin da kasashen duniya ke ciki game da annobar ya fitar cewa ana cigaba da samun hau-hawan yawan mutanen dake kamuwa da cutar a kasar Amurka da kuma wadanda ke rasuwa a kullum.

A makon da ya gabata akalla mutum 1,167 suka mutu a cikin uni daya.

A yanzu dai Amurka ita ce kan gaba wajen samun yawan mutanen da korona ta kashe a duniya.

Mutum miliyan 11.8 me suka kamu da cutar Amurka a yanzu haka.

A yanzu mutum miliyan 56 ne suka kamu da cutar sannan miliyan 1.3 sun mutu a duniya.

Share.

game da Author