“Idan ka na cikin jam’iyyar da ba ita ke mulki ba, kai ma ka san azumin da babu lada ne kawai ka ke dauke da shi, kullum yunwa na cin ka. Ko dai ka ci gaba da azumin har Allah ya karbi addu’ar ka, ko kuma yunwa ta kashe ka a banza.”
Wannan ne shaguben da Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ya yi wa masu adawa, yayin da ya ke kiran su da kowa ya zo ya shiga jam’iyyar APC.
Ya yi wannan jawabi a Abuja, a lokacin da ya ke magana dangane da komawar Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi daga PDP zuwa APC.
Da ya ke zantawa da manema labarai bayan ganawar sa da Shugaba Muhammadu Buhari, Uzordinma, y ace masu David Umahi ya koma APC ne bayan ya gano cewa idan bai koma jam’iyyar mai mulki ba, to al’ummar jihar Imo za su ci gaba da kasancewa cikin yunwa.
“In dai kai cikakken dan Nanjeriya, to kamata ya yi kawai ka bi jam’iyya mai mulki.cdomin idan ka ce za ka ci gaba da adawa, to sai dai ka yi ta zama cikin yunwa, ka na dauke da azumin da babu lada, har sai ranar da Allah ya karbi addu’ar ka. Ko kuma ka juri zama cikin yunwa har ta kashe ka.”
“Amma idan mu na cikin jam’iyya mai mulki, za mu fi saurin warware matsalolin mu, fiye da a ce mu na can nesa da inda mulki ya ke, wato gindin maganin abin sosai.”
Wannan magana ta gwamna Uzodinma na nufin gwamnatin Buhari na fifita jihohin da APC ke mulki fiye da na PDP wadaanda ba ita ke mulkin su ba.
Sannan kuma ya na nufin siyasar Najeriya babu sauran kyakkyawar akida a ciki, duk bankaura da nuna bambanci ake yi akwai.
Uzodinma ya yi kiran sauran gwmnonin jihohin Kudu maso kudu su bi hanyar da gwamnan Imo David Umahi ya bi, ya fice daga PDP, ya koma APC.
Discussion about this post