Wani mazaunin kauyen Dakaiyawa dake karamar hukumar Kaugama, jihar Jigawa, ya daba wa saurayin tsohuwar matar sa wuka da yayi sanadiyyar rasuwar sa saboda tsananin kishi.
Tsohon mijin mai suna Umaru ya bi saurayin tsohuwar matarsa har inda yake, sannan ya caka masa sharbebiyar wuka saboda tsananin kishin wai yana tadi da ita, duk da ya sake ta.
An gano cewa, Umaru ya saki matar sa da kwana uku sai sabon saurayi ya bayyana, ashe hirar ajali yake yi.
Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Jigawa ya tabbatar da aukuwar wannan kisa inda ya kara da cewa tuni yan sanda sun fantsama wajen farautar Umaru.
” Ko da jami’an mu suka isa wurin da Umaru ya aikata kisan, mun samu Sale Dange mai shekaru 45 kwance male-male cikin jini. Sai dai likitoci sun tabbatar da ya rasu bayan an kai shi asibiti.