Kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ya bayyana cewa manoman da Boko Haram suka yi wa kisan gilla, ganganci suka yi da suka kai kansu wannan gonan shinkafa.
Garba Shehu ya ce tun farko bai kamata manoman su yi gaban kansu ba su tafi yin aiki a wannan gona ganin nan wurare ne dake da tsananin matsalar tsaro.
Shehu ya fadi haka da yake hira da BBC ranar litini.
Sai dai kuma Shehu ya ce ba wai yana nuna rashin damuwarsa bane game da kisan da aka yi wa manoman, abin nda ya ke nufi shine bai kamata su tafi wannan gona ba tare da sun samu izinin jami’an tsaro ba, domin wadannan wurare ne dake da tsananin rashin tsaro.
Sannan kuma akwai bama-bamai na kasa da aka bibbine a wuraren da dole sai an samu izinin sojoji kafin mutane su garzaya wuraren.
” Ƴan kasuwa, jami’an gwamnati da ma’aikatan agaji na majalisar dinkin duniya duk sai sun nemi izinin jami’an tsaro kafin su tafi ire-iren wadannan wurare saboda rashin tsaro.
” Babu wani da ke murnar abin da ya faru a Zabarmari, saboda haka bai dace a rika yi wa kalamai na mummunan fassara ba arika maida shi siyasa ba.
Boko Haram sun yi wa wasu manoman shinkafa 43 kisan gilla a daidai suna girbi a kauye Zabarmari, dake jihar Barno.
Maharan sun yi musu zobe ne sannan suka rika bi suna bude musu wuta.
Wannan abu ya tada wa ƴan Najeriya hankali, kuma kwatsam sai gashi fadar shugaban kasa, ta bakin kakakin fadar Garba Shehu ta na cewa wai manoman sun yi gangancin zuwa wannan wuri ne.
Sakon Zulum ga Shugaba Buhari
Gwamnan jihar Barno ya shawarci tawagar gwamnatin tarayya da suka kawo masa jaje, da yi masa ta’aziyyar kisan gillan da Boko Haram suka yi wa manoma sama da 40 a kauyen Zabarmari.
Tawagar gwamnatin Tarayya ta isa garin Maiduguri ranar Litini to inda ta gana da gwamnan jihar Babagana Zulum.
A jawabinsa Zulum ya shawarci gwamnatin tarayya ta yo hayan zaratan sojoji daga kasashen waje su zo su gama da Boko Haram tunda abin yaki ci yaƙi cinyewa.
Daga nan sai ya ba gwamnati shawara kamar haka:
1 – Ga dubban matasa nan da basu da abin yi, me zai hana Gwamnati daukan su aikin soja da ɗan sanda ba domin kara yawan jami’an tsaro a kasar nan.
2 – Gwamnati ta nemi hadin kai da taimakon gwamnatocin kasashen dake makwabtaka da Najeriya domin kakkabe sauran maboyan Boko Haram dake kan iyakokin kasashen.
3 – Sannan kuma ina kira ga gwamnati ta dauko hayan sojoji daga waje su shigo su kakkabe sauran maboyan Boko Haram dake Sambisa, su share mana ita tas.
4 – Gwamnati ta samar wa jami’an tsaro da manyan motocin yaki da kuma makamai masu masu nisan zango na zamani.
5 – Muna kira ga gwamnatin tarayya ta agaza wa jihar domin dawo da ƴan asalin ƙasar har dake zaman gudun hijira a kasashen Kamaru, Nijar da Chad, su dawo gida hakanan.
6 – Ina rokon gwamnatin tarayya ta kawo ayyukan cigaba a jihar Barno, cewa gwamnati ta yi watsi da jihar babu wani aikin cigaba da take yi a kasar har.
Ya ce rashin ababen more rayuwa ma na daga cikin abubuwan da ke ci wa gwamnati tuwo a kwarya a jihar.
” Baya ga shekara 11 da jihar ke fama da hare-haren Boko Haram, yanzu kusan shekara 25 kenan rabon da ace wai gwamnatin tarayya ta kawo wani aikin cigaba, cikin jihar Barno, da wasu jihohin Arewa maso Gabas.
” Idan da gwamnatin tarayya za ta iya gyara titunan jihar da za a samu sauki matuka.
A nashi jawabin, jagoran tawagar gwamnatin tarayya, Shugaban majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya ce Buhari ya nuna rashin jin dadin sa ga kisan gillan da aka yi wa wadannan manoma.
Sannan kuma ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiki tukuru domin ganin an kawo karshen wannan ta’addanci na Boko Haram da rashin tsaro da ya addabi ƴan Najeriya.
Tawagar gwamnati tarayyar ya hada da shugaban gaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno da wasu manyan jami’an gwamnati.