KISAN MANOMA: Kungiyar Manoma ta nemi a markade Dajin Sambisa, a maida shi fili

0

Kungiyar Manoma ta Najeriya ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta dau kwakkwaran mataki a kan Boko Haram, ta hanyar kakkabe Dajin Sambisa, a markade shi, a maida shi sarari gaba daya.

Kungiyar ta ce kisan kiyashin da Boko Haram su ka yi wa manoma a ranar Asabar a Zabarmari, ya zama wata babbar barazana ga harkar noma da samar da abinci a kasar nan.

Kungiyar ta ce ya kamata a kwantar da duk wata bishiya, a markade Dajin Sambisa da katafiloli, domin a kawar sa surkukin dajin da Boko Haram ke boyewa tsawon shekaru goma kenan, ko ma fiye.

Wannan kiraye-kirayen dai ya biyo bayan da “yan ta’addar da ake ganin Boko Haram ne su ka danne manoman shinkafa har guda 43, duk su ka yi masu yankan rago.

Wannan ta’addanci dai an fassara shi a matsayin ta’addanci mafi muni a cikin wannan shekara a duniya.

Cikin wata takarda da kungiyar ta manoma ta fitar a ranar Litinin, Shugaban Kungiyar Manoma ta Kasa, Kabiru Ibrahim ya ce, “tilas gwamnati ta dau nauyin kakkabe wannan matsalar duk wani munin da ba so ta kai ko ba a zaton za ta kai, tuni ta kai.

Shugaban na AFAN ya ce, “harkar noma a kasar nan ta na cikin wasifa. Ma kuma abin da ya faru da manoman nan su 43 a Zabarmari, ya kara tabbatar da cewa harkar noma da bunkasa kasa da abinci ya shiga garari, kuma ya samu tawaya gagarima. Don haka babban abin yi a kokarta ganin an shawo kan matsalar kawai.” Inji shugaban na AFAN.

Harkar noma da bunkasa abinci ta samu kan ta cikin mawuyacin hali bayan barkewar cutar korona da ambaliya sa kuma uwa-uba wannan yankan rago da aka yi wa manoma 43 a Barno.

AFAN ta ce kowa ya san Boko Haram sun samu mafaka da wurin bajekolin su a cikin Dajin Sambisa. Don haka a share dajin baki dayan sa domin a samu nasarar fatattakar Boko Haram a yankin.

Share.

game da Author